Zainab matashiya ce yar kimanin shekara 18 da haihuwa, ba fara ba ce sosai (chocolate color) ce, tana da manyan idanuwa, bakinta daidai misali, hancin ta ma daidai misali. Faffadar fuska gareta, me matsakaicin tsayi ba tada kiba sosai amma kuma ba za a kirata da siririya ba, tana da kyan diri. Zainab dai ba laifi tana da kyanta, don ta hada dukkanin abubuwan da ake bukatar ganin ‘ya mace da shi.
Bangaren ilmi ma ba a bar ta baya ba, domin Zainab tana da Ilmin addini da na zamani. Ba ta wasa wajen zuwa Islamiyya, inda kusan duk shekara ita ke kan gaba a jarabawa. Har ila yau a makarantar boko, tuni ta kammala Sakandire a Kano Royal Academy.
Mahaifinta Alhaj Tukur Abdullahi attajiri ne, wanda ya shahara sosai kasancewar Allah ya yi masa arziki. Ya rasu tun Zainab na karama ita da kanwarta Habiba. Ya bar mahaifiyarsu Hajiya Sakina tare da yayansu; Mustapha, wanda suke kira da Yaya Musty.
Mahaifinsu dan asalin Jihar Kaduna ne, mahaifiyarsu kuma ‘yar asalin garin Birnin Kudu ce, yanayin kasuwancinsa ne ya sa shi zama a garin Kano har yayi aure ya haifi ‘ya’ya, kafin Allah ya dauki ransa.
Zainab na da aminiya da ake kira Khadija, amma an fi yi mata lakabi da Precious. Tare suka kammala makaranta sun shaku da juna sosai.
Ranar wata Asabar da rana suka hadu a bikin Imaan Habib, kawarsu ce wadda ita ma suka gama makaranta tare. A duk lokacin da suka hadu Precious takan bawa Zainab labarin saurayin da ta hadu da shi. Yanzun ma labarin Saif din ne ta cigaba da yi mata shi, tana yaba haduwarsa. Takan ce “Saif yana da kyau sosai, ga shi ya iya kwalliya, rayuwarsa tana burge ni”.
Babban abinda ya fi daukar hankalin Precious kan Saif bai wuce iya kwalliyarsa da kuma kyan da Allah ya yi masa ba, wannan ya sa take kasa jure fadansa a koyaushe.
Cikin mamaki Zeey Colour ta kalli Precious a hankali kuma ta saki wani irin murmushi tare da cewa, “Ke dai har yau labarinki ba ya wuce na Saif.” Murmushi Precious ta yi me kwantar da zuciya ta ce, “Hmm.! Ai don ba ki gan shi bane, kin ji wani suna ma da suke fada masa?”
Ita dai Zainab ta zuba mata ido tana kallon ta kawai a hankali, sannan ta ce, “sai kin fada” Precious ta dada gyara zama ta ce “Usy Mam suke ce masa, kin ga yanzu ma har na karbi wata lambar.”
Zainab dai abun mamaki yake ba ta sai dai kuma ba ta nuna mata bakin cikin hakan ba sai na kuskuren da ta yi.
Samfurin Kalaman Soyayya
MASOYIYA
Masoyiyata a duk lokacin da na ji muryar ki nakan samu natsuwa a zuciyata.
Murmushinki gare ni ya fi a bani kyautar sabuwar mota da gida.
Fuskarki a kullum haske take kara yi musamman idan kina murmushi, Idan ki ka yi fushi sannan ne kike dada kara kyawun gani.
MASOYI
A kullum bani da burin sauraren wani zance idan ba naka ba.
Kai ne wanda ka dace da sarautar zuciyata don haka na baka ita kyauta.
Zan iya aiwatar da komai har idan ina jin kalamanka masu sanyaya zuciya,
Na yarda da kai na aminta da kai don haka