Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home ADON GARI

Labarin Zainab Da Mubarak

by Tayo Adelaja
September 16, 2017
in ADON GARI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Zaune Zainab take kan kujerar da ke makeken falo wanda aka kawa tashi da kayan kyale-kyale, idanuwanta na kan talabijin kirar zamani (Plazma) da aka dire daga gefe tana kallon wani Indian fim mai suna ‘Dil Ka Kya Kusoor’.

Wayarta kirar Tecno da ke gefen teburi ce ta fara kadawa, da sauri ta kai hannu ta dauki wayar sai dai kuma ba ta san wanda ya kira ta ba, don lamba kawai babu suna, amma haka ta latsa wayar ta kai kunnenta.

Sallama ta fara yi tare da fadin “wa ke magana?” Wata murya ta ji me sanyi da ratsa zuciya ga duk wanda ya ji ta dole ne zuciya ta kwanta, hakan ne ya dada kayatar da ita har ta kagu ta ji me yake son furtawa.

A hankali ta ji an ce, “ba ki gane me magana ba?” Ta dan nisa kadan tare da murmushi ta ce “a’a ban gane me magana ba.” Ya yi murmushi sannan ya ce, “Da gaske ba ki gane me magana ba?” Ita ma murmushin ta yi “da gaske nake ban gane ba”, ya dada nisawa sannan ya ce “Yaya kuwa ya zaneki bayan da kika koma gida?”.

Dariya ta farayi sannan ta yi ajiyar zuciya, don kuwa ta yi imani babu wanda zai kirata ya fada mata haka face Mubarak, da sauri ta kawar da wannan tunani suka cigaba da hira.

“Ai bayan da na koma gida na sha duka sosai a wajen Yaya”, ta dada kyalkyalewa da dariya, har zuciyarsa yana jin dadin yadda take masa magana saboda ta iya hira, kalamanta na kara sa shi nishadi ji yake tana kara shigar masa rai, ya yi dariya ya ce “Da wacce bulalar ya doke ki?”, murmushi ta yi sannan ta ce “Ai ba da bulalar da be dake ni da ita ba, har da ma me baki biyu, da na san hakan ne zai kasance da tun a kasuwar zan baka hakuri”.

Ya dada kyalkyalewa da dariya, shi dai tana burge shi musamman yanayin yadda take masa magana yana jin dadin kalamta sosai.

Murmushin da ta yi shi ya kawar da tunanin da yake yi a kanta.

Ya dada kwantar da murya “Amma yaya bai kyauta ba, ya yi dukan da yawa”. Cikin sanyayar murya ta ce, “Har ma sai da aka yi min gashi”. Nan ma ya sake kyalkyalewa da dariya sannan ya ce, “Toh! Ya gida? Ya kuma kuka je gida”. “Lafiya lau” ya ce masa, kafin daga bisani ya dora zancensa da cewa, “Na dade ina cewa Humaira ta bani lambarki amma sai ta ce min wai babu a wayarta bayan kuma na san karya take yi”.

Tsuke fuska Zainab ta yi duk da ba kallonta yake ba ta saukar da murya, “kawar tawa ce take karya?” Ya yi murmushi “A’a! mantawa na yi gan-gan take min kin san manya basa karya”.

Ita kanta yana burge ta, kalamansa suna mata dadi hirarsa na kayatar da ita. Ta rausayar da kai tare da murmushi, sai dai kuma ba ta ce da shi kala ba, sai ya ci gaba da magana, “ko ba haka ba ne?” Ta dada langwabewa jikin kujera sai ka ce mage ta ce “Ni na isa in ce ba haka ba, rufa min asiri!” Tare suka yi murmushi tamkar suna kallon juna, kafin daga bisani Mubarak ya ce, “yanzu bari na bar ki don na san duk na dame ki da surutu.” Ya dan zolaye ta.

Abinda ta lura da shi ya iya barkwanci, ta nisa kadan tare da ajiyar zuciya ta ce “ko kadan ba ka dame ni ba, sai dai ma ni nake ganin kamar na dame ka”, ya ce “ko kadan ba na jin hakan za ta iya faruwa, ina so ki cire wannan tunanin daga kwakwalwarki”.

Ta yi farin ciki da abinda ya fada mata ta ce “Ba zan kara ba.” hade da murmushi ta yi maganar. Mubarak ya langwabar da kai tare da furta cewa, “Na ji dadin hakan, bara na bar ki kar na sa ki yi laifi. Ta ce “laifi kuma, kai dai ka fiya zolaya”. Yayi murmushi suka yi sallama ta kashe wayar.

Bayan sun gama waya, ta janyo matashin kai da ke gefen kujera ta dora kan cinyarta tare da rungume hannayenta akansa, tana dada tunano yanayin yadda Mubarak yake mata magana. Hirarsa ta burge ta sosai, har zuciyarta tana ji duk duniya babu wanda ya kwanta mata kamar Mubarak, don ya iya hira mai dadi har ya kansa mutum ya manta da komai sai dai kuma har yanzu tana jin sautin muryarsa na mata rada a kunne. Ta yi murmushi ta dada gyarawa tare da lumshe idanuwanta, lokaci guda kuma ta bude su kadan.

Zan ci gaba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Mene Ne So, Soyayya, Shakuwa?

Next Post

Muhimmancin Kalaman Soyayya

RelatedPosts

Na Shiga Siyasa Ne Don Gyarawa Maza Taku A Jihar Kaduna – Inji Aisha Galadima

Na Shiga Siyasa Ne Don Gyarawa Maza Taku A Jihar Kaduna – Inji Aisha Galadima

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Daga Amina Bello Hamza Na Shiga Siyasa Ne Don Gyarawa...

Yana Da Kyau Mata Su Rika Hada Aure Da Karatu Da Sana’a – Munira Suleiman

Yana Da Kyau Mata Su Rika Hada Aure Da Karatu Da Sana’a – Munira Suleiman

by Muhammad
6 days ago
0

Daga Umar Muhsin Ciroma, Hajiya Munira Suleiman Tanimu, ta kasance...

Dogaro

Dogaro Da Kai Shi Ne Abu Mafi Daraja Ga ‘Ya Mace – Amrah Mashi

by Muhammad
1 week ago
0

Bakuwarmu ta Adon Gari a wannan makon ta yi bayanin...

Next Post

Muhimmancin Kalaman Soyayya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version