Labaru 7 Da Ke Bayyana Yadda Xi Jinping Yake Kulawa Da Kananan Yara Na Kasar Sin

Daga Tasallah Yuan,

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba ambato cewa, babban burinmu shi ne ganin kananan yara manyan gobe sun girma yadda ya kamata. Kullum yana mai da hankali kan yadda yara manyan gobe suke girma kamar yadda ake fata. Ya sha kai rangadin aiki a makarantu, da ganawa da yara cikin halin aminci da nuna musu fatansa. Bayanansa da abubuwan da ya yi, sun nuna yadda yake kulawa da yara manyan gobe na kasar Sin a matsayinsa na abokinsu.

Yara su ne manyan gobe na ko wace kasa. Al’ummar Sinawa kan nuna musu kyakkyawar fata. A jajibirin ranar yara ta kasa da kasa da ake bikinta a ranar 1 ga watan Yunin shekarar bana, bari in gabatar muku labaru guda 7 kan yadda shugaba Xi Jinping yake kulawa da yara manyan gobe na kasar Sin.

Kasar Sin ba za ta bunkasa ba, sai yara manyan gobe sun inganta kwarewarsu. Har kullum shugaba Xi Jinping yana mai da hankali kan yadda matasa da kananan yara manyan gobe suke girma yadda ya kamata. Ya sha jaddada cewa, dole ne iyalai, makarantu da sassa daban daban na zamantakewar al’ummar kasa baki daya, su samar wa kananan yara manyan gobe sharadin inganta lafiyarsu, a kokarin ganin sun girma kamar yadda bishiyoyi suke girma, su kuma zama ginshikan kasar Sin a nan gaba.

Ranar 21 ga watan Afrilun shekarar 2020 da safe, kananan yara manyan gobe daga makarantar firamare na garin Laoxian dake gundumar Pingli a birnin Ankang na lardin Shaanxi sun sadu da kaka Xi Jinping a dakin karatunsu. A dakin karatun, shugaba Xi Jinping ya yi musu tambayoyi dangane da harkokin karatunsu da yadda suke rayuwa. Ya kuma nuna cewa, yanzu ana kara samun yara dake amfani da tabarau saboda ba sa iya gani sosai. Wannan ya dame shi. Haka kuma ya damu da lafiyarsu. Ba su motsa jiki sosai, ba su da lafiyar jiki kamar yadda ake fata. Wajibi ne a wayar musu da kai da kuma inganta lafiyarsu, dole ne a tabbatar sun yi motsa jiki sosai. Daga bisani shugaban kasar Sin ya je dakin cin abinci na makarantar, inda ya kalli irin abincin da yara suke ci da kuma yadda aka dakile da kandagarkin yaduwar annobar numfashi ta COVID-19, bayan an dawo da harkokin karatu a makarantu. Ya kuma bukaci a kara kashe kwayoyin cuta a wasu muhimman sassan makarantar, a kokarin inganta yanayi ga malamai da kananan yara.

A gabannin “Ranar Yara Manyan Gobe Ta Duniya” ta ranar 1 ga watan Yuni, Xi Jinping ya kan amsa wasikun da yara suka aiko masa, inda ya karfafa gwiwarsu kishin kasa da kaunar jama’a.

A ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2019, Xi Jinping ya amsa wasikar da ’yan makarantar firamare ta Yingcai a yankin musamman na Macao suka aiko masa, inda ya ce, “Sannunku! Na samu wasikarku. Zane-zanenku na da kyan gani sosai. Kun rubuta min wasikar cikin sahihanci, wadda ta nuna kyan zukatanku.” Kana ya taya su da ma daukacin yaran kasar Sin murnar “Ranar Yara Manyan Gobe Ta Duniya”.

Daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2021, Xi Jinping ya kwashe shekaru 9 a jere yana dasa bishiyoyi a birnin Beijing. A ranar 8 ga watan Afrilun shekarar 2019 ne ya dasa bishiyoyi tare da yara a garin Yongshun dake yankin Tongzhou a Beijing. Yayin da yake dasa bishiyoyi, ya yi wa kananan yaran da suke tare da shi tambaya game da karatunsu, zaman rayuwarsu da yadda suke motsa jiki a kullun. Shugaban ya nuna musu fatansa na ganin sun mai da hankali kan kiyaye muhallin halittu tun suna kanana, kana sun kara raya kasar ta Sin mai kyan gani da hannunsu. Ya kuma yi fatan cewa, za su girma yadda ya kamata kamar yadda bishiyoyi suka girma.

A ranar 9 ga watan Satumban shekarar 2016, shugaba Xi Jinping ya ziyarci makarantar Bayi da ke birnin Beijing, inda ya taba karatu a baya. Ya gana da malamai da ’yan makarantar cikin halin aminci. A cibiyar fasaha dake makarantar, ya shiga dakin gwaje-gwajen kimiyya, inda ya saurari darasin da ya shafi kananan taurarin dan Adam, wanda makarantar Bayi da cibiyar mu’amalar kwararru masu ilmin sararin samaniya na kamfanin kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin suka gudanar cikin hadin gwiwa. Shugaban ya kuma duba samfurin tauraron dan Adam da dai sauransu, tare da yin mu’amala da malamai da ’yan makarantar. Har ila yau a ranar 24 ga watan Disamban shekarar 2016, ya amsa wasikar da kungiyar nazarin kananan taurarin dan Adam ta makarantar Bayi ta aiko masa, inda ya yi fatan cewa, wannan karamin tauraron dan Adam zai ba da jagora wajen karfafa gwiwar yara kara kuzari kan binciken kimiyya.

A ranar 3 ga watan Agustan shekarar 2014, an yi girgizar kasa mai karfin maki 6.5 a gundumar Ludian a yankin Zhaotong dake lardin Yunnan a kudu maso yammacin kasar Sin, wadda ta haddasa mummunar asarar rayuka da dukiyoyi da ababen more rayuwar jama’a a wurin. Bayan abkuwar bala’in, nan da nan shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurnin tsugunar da mutanen da bala’in ya rutsa da su yadda ya kamata da gudanar da ayyukan sake gina wuraren da bala’in ya shafa. A watan Janairun shekarar 2015, ya kai rangadin aiki a Yunnan, inda ya gana da jami’ai da al’ummomin da bala’in ya shafa a Ludian. A matsugunin mutanen da bala’in ya shafa a kauyen Ganjiazhai, Xi Jinping ya shiga tsakanin yara a dakin gudanar da harkokin kananan yara, ya rike hannunsu, tare da duba zane-zanen da suka yi, ya yi fatan cewa, za su girma yadda ya kamata.

A ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2014, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara makarantar firamare ta Minzu da ke yankin Haidian na birnin Beijing, inda ya halarci bikin murnar ranar kananan yara ta kasa da kasa ta ranar 1 ga watan Yuni. Tare da rakiyar kananan yara, Xi Jinping ya sake halartar bikin shiga kungiyar yara ta Kwaminis ta kasar Sin. Ya gaya wa kananan yaran da ke kewayensa cewa, “Na fara karatu a makarantar firamare a shekarar 1959, na zama dan kungiyar yara ta Kwaminis ta kasar Sin a shekarar 1960. Ban zama dan kungiyar a rukuni na farko ba saboda ina karami a wancan lokaci. Na yi kuka.” Da jin haka, yaran sun yi dariya. Daga baya Xi Jinping ya ci gaba cikin murmushi da cewa, “Ko martaba ta ta zube?” Yaran sun amsa cewa, “E, haka ne!” Xi Jinping ya nuna musu cewa, “Na ga kyakkyawar fata a fuskokinku. Kasar Sin da al’ummomin Sinawa mun nuna muku kyakkyawar fata. Kamar yadda muka yi alkawari dazun nan, wajibi ne, ku shirya don maye gurbinmu a fannin ci gaba da raya kasarmu ta Sin.”

A ranar 29 ga watan Maris na shekarar 2014, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya je filin wasan kwallon kafa na babban filin wasanni na Olympia da ke birnin Berlin, hedkwatar kasar Jamus, a lokacin da yake ziyarar aiki a kasar. Mambobi 20 na kungiyar wasan kwallon kafa ta yara daga gundumar Zhidan dake lardin Shaanxi a arewa maso yammacin kasar Sin, sun samu horo tare da takwarorinsu daga kungiyar wasan kwallon kafa ta Wolfsburg a karkashin jagorancin wani mai horas da ’yan wasa na Jamus. Xi Jinping ya zauna a dandamalin ’yan kallo, daga baya an fara gasa a tsakanin ’yan wasan kwallon kafan yara na kasashen Sin da Jamus. Xi Jinping ya kalli gasar tare da sauraron abubuwan da aka gabatar masa dangane da yadda wadannan yara ’yan wasan kwallon kafa na kasar Sin suka samu horo a Jamus. A hutun rabin lokaci na wasan, Xi Jinping ya shiga tsakiyar ’yan wasan kwallon kafar na kasar Sin, tare da gaya musu cewa, “Yanzu kuna samun horo a Jamus, ina fatan za ku ba da jagora ga takwarorinku na kasar Sin.” Haka kuma ya yi fatan cewa, karin kananan yara da matasa za su dukufa wajen raya sha’anin wasan kwallon kafa na kasar Sin. Ya nuna musu fatan alheri, da ma takwarorinsu na kasar Sin. Ya kuma yi fatan cewa, nan gaba yaran za su zama fitattun ’yan wasan kwallon kafa. (Tasallah Yuan)

Exit mobile version