Labarun Shugaban Kasar Sin Game Da Kawar Da Talauci

“Muna cike da imanin cewa, za mu kafa al’umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni kamar yadda aka tsara, da tabbatar da kawar da talauci

Daga CRI Hausa

“Muna cike da imanin cewa, za mu kafa al’umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni kamar yadda aka tsara, da tabbatar da kawar da talauci a kauyuka bisa ma’unin da muke bi a yanzu, kana da cimma burin rage talauci bisa “Ajandar Neman Dauwamamman Ci Gaba nan da Shekarar 2030 na MDD ” kafin shekaru 10 da ake zato.

“Muna cike da imanin cewa, za mu kafa al’umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni kamar yadda aka tsara, da tabbatar da kawar da talauci

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da haka ne ga duniya baki daya a yayin muhawarar babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 75 da ya gudana a ranar 22 ga Satumban shekarar 2020.

A yayin da ya halarci babban taro na Majalisar Dinkin Duniya karo na 70  da kuma ziyara a Amurka a shekarar 2015 shekaru biyar da suka wuce, Xi Jinping ya gabatar da jawabi a birnin Seattle na Washington, inda ya bayyana burinsa sama da shekaru 40 da suka wuce, wato “Abu guda da nake fatan cimmawa shi ne, mazauna kauyuka za su iya cin nama har su koshi, kuma kullum su rika cin nama.”

A lokacin da yake aiki a kauyen Liangjiahe dake birnin Yan’an na Lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin, inda ya kalli wahalhalun da mazauna wurin suke fuskanta, yanayin yakar talauci da ake ciki a yankunan karkara na kasar Sin ya bai wa Xi Jinping wani abin da ba za a manta da shi ba.

Manyan rumfunan shuke-shuken fungus da aka kafa a Zhashui

“A cikin shekaru 40 da wani abu da suka gabata, na yi aiki a yankunan a matsayin gundumomi, birane, larduna, da kuma kwamitin tsakiya. Ko da yaushe kawar da talauci ya kasance wani muhimmin sashe na aiki na, wanda kuma ya fi jawo hankali na.”

Daga sakataren reshen jam’iyya na kungiyar samar da kayayyaki a kauye zuwa shugaban babbar kasa, kullum Xi Jinping yana damuwa da mutane masu fama da talauci, kuma yana daukar nauyin kawar da talauci dake wuyansa.

Yanzu, burin da ya cimma a shekaru masu yawa da suka gabata ya cika. Ya zuwa karshen shekarar 2020, kasar Sin ta kawar da talauci a tsakanin mutanen da kudin shiga da suka samu ba su iya biyan bukatun zaman rayuwarsu a kasar baki daya ba, har ta zama kasar da ta fi samun yawan al’umma da aka kawar daga talauci a duniya.

Ga wasu labaru masu burgewa game da Xi Jinping, wadanda ke bayyana alakar dake tsakanin shugaban kasa da ayyukan da yake kokari na kawar da talauci……

Dogon rami na hanyar mota ta Dulongjiang

Bunkasa fungus zuwa matsayin manyan masana’antu

Fungus amfanin gona ne da mutanen Zhashui na lardin Shaanxi suke nomawa tun zamanin daular Qing. Amma, saboda yadda ake amfani da hanyar noma ta gargajiya wajen noma irin wannan amfanin gona, don haka, da kyar ake iya samun ci gaba a fannin na tsawon lokaci. A yanzu dai, shuke-shuken fungus ya zama sana’ar dake jagorantar mazauna wurin wajen samun wadata. A watan Afrilu na shekarar 2020, lokacin da Xi Jinping ke binciken yanayin kawar da talauci a gundumar Zhashui, ya nuna yabo cewa, “Karamin fungus, amma babbar sana’a ce”, wato ana raya karamin amfanin gona har ya kasance wata babbar sana’a.

A baya kauyukan da ke fama da talauci a gundumar Zhashui sun kai kimanin 79, mazauna wurin dake shan matukar wahala sakamakon talauci sun tsaida kudurin kawar da talauci ta hanyar amfanin gona na fungus da suke nomawa.

Gundumar Zhashui ta yi mu’amala da malama Li Yu, masaniya a wannan fannin ta kasar Sin. Bayan binciken da ta yi, malama Li Yu ta zabi nau’ikan fungus 4 don yada su a duk gundumar. Daga baya kuma, an soma kafa manyan rumfunan shuke-shuken fungus.

Mazauna kauyen Yuangudui na Lardin Gansu suna shuke-shuke

Bayan shekaru kusan 3 da suka gabata, ta hanyar kimiyya da fasaha an raya ayyukan da suka shafi fungus da ya zama wata babbar nasara, kuma sannu a hankali aka kafa wani tsarin sana’a da ya kunshi binciken iri, noma, sarrafa fasaha, rarraba da daure kaya, adanawa da jigilar kaya, da sauransu.

Yanzu haka, baki dayan iyalan dake samun tallafi da yawansu ya kai kusan 7000 a gundumar Zhashui, sun shiga ayyukan da suka shafi sana’ar fungus,  kuma matsakaicin kudin shiga da ko wane gida ya samu ya karu da yuan 5,000 da wani abu a ko wace shekara.

Nuna fatan alheri a sabuwar shekara

Ranar bikin bazara rana ce da Sinawa ke haduwa tun fil azal.

Yaya masu fama da talauci suke a bikin bazara? A gabannin bikin bazara na ko wace shekara, Xi Jinping da kansa ya kan ziyarci yankunan da ke fama da talauci.

A jajibirin bikin bazara na shekarar 2013, Xi Jinping ya ziyarci gidan dattijo Ma Gang, dake kauyen Yuangudui na gundumar Weiyuan ta birnin Dingxi dake lardin Gansu.

“Tsoho Ma, shekarunka nawa? Ina maka gaisuwar sabuwar shekara.” Suna haduwa, sai Xi Jinping ya rike hannun Ma Gang ya kuma nuna masa fatan alheri. Bayan ya duba karamin gida da yake ciki wanda ya lalace, Xi Jinping ya yi tambaya cikin damuwa cewa, “Yaushe aka gina gidanku? Shekaru nawa kuke zaune a nan?”

Da yake tuna abin da ya faru a lokacin, Ma Gang ya ce, “Babban sakatare ya shiga gida na, kuma ya zauna a kan gado ba tare da la’akari ko yana da tsabta ko a’a ba, bayan haka sai ya fara hira da ni.”

Karancin ruwa da fari babbar matsala ce da ke addabar yankin wajen kawar da talauci.  Da Xi Jinping ya ga tankin ruwa a cikin gidan, da gangan ya debo ruwa kuma ya sha kadan, daga baya ya murtuke fuska.

Mazauna kauyen Zhashui suna tsintar fungus

A rana ta biyu, Xi Jinping ya yi tattaki na musamman zuwa wurin aikin samar da ruwan sha na gundumar don duba yanayin aikin ginin, sannan ya umarci jami’an wurin da na hukumomin da aikin ya shafa, da su yi kokari don ganin mazauna wurin sun samu shan ruwa mai tsabta da gardi nan da nan.

A cikin shekaru 7 da ya shafe yana aiki a kauyen Liangjiahe, Xi Jinping yana da Imani a tsawon rayuwarsa: za a fitar da wurare da yawa kamar Liangjiahe da ke kasar Sin daga talauci da wuri-wuri.

A jajibirin bikin bazara na shekarar 2015, Xi Jinping ya koma kauyen Liangjiahe tare da daukar kayayyakin sabuwar shekara da ya sayawa mazauna wurin. Lokacin da yake hira da mazauna wurin da ba su hadu da juna ba har tsawon shekaru 40, ya ce, “Ba zan manta da Liangjiahe ba, kuma ba zan manta da jama’ar dake nan ba.” Ya kuma ce, “Barka da sabuwar shekara, kuma ina yi muku fatan alheri da farin ciki da samun wadata, a sabuwar shekara.”

Yayin da ya ziyarci gidajen mutane masu fama da talauci, Xi Jinping ya kan tambaye su yadda suke samun abinci, kudin shigar da suka samu, nawa suke kashewa wajen ganin likita, nawa suke kashewa wajen biyan kudin makaranta… Wannan shi ne Xi Jiping, shugaban kasa dake daukar masu fama da talauci a matsayin dangoginsa.

Labarin wasikar da ya amsa

A yammacin ranar 20 ga watan Janairu na shekarar 2015, Xi Jinping, wanda ke yin bincike a birnin Kunming na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, ya shiga dakin taron na otel din da yake zaune, inda wasu wakilan jami’ai da mazauna gundumar mai cin gashin kai ta Gongshan ta kabilun Dulong da Nu suke jira don ganawa da shi.

Xi Jinping ya ziyarci gidan dattijo Ma Gang, dake kauyen Yuangudui

A shekara daya da wani abu da ta gabata, jami’ai da mazauna gundumar Gongshan sun rubuta wa shugaba Xi Jinping wata wasika, inda suka ce, ana daf da kammala aikin dogon rami na hanyar mota ta Dulongjiang dake tsaunin Gaoligong yana gab da kammala. Bayan karbar wasikar, nan ta ke Xi Jinping ya ba su amsa cewa, “Ina taya ‘yan kabilar Dulong murna!” A cikin wasikar, ya kuma bayyana fatan cewa, jama’ar Dulong za su “hanzarta kawar da talauci da samun arziki, ta yadda za su yi zaman rayuwa cikin wadata tare da sauran ‘yan uwa a fadin kasar baki daya nan da nan”

Bayan shekara fiye da guda, yaya aka gina dogon ramin hanyar mota ta Dulongjiang? Wadanne canje-canje aka samu a zaman rayuwar ‘yan kabilar Dulong? Domin tunanin mazauna kauyen, a yayin da yake ziyarar gani da ido a wurin, Xi Jinping ya tarbi wadancan jami’ai da talakawa wadanda suka rubuta masa wasika a Kunming.

Xi Jinping ya yi tambaya cewa, “Wane tsawon lokacin za a dauka don fita daga wannan tsauni?”

Gao Derong, tsohon shugaban gundumar, ‘dan kabilar Dulong, ya ce, kafin kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin, ‘yan kabilar su kan shafe rabin wata suna kai da komawa ta hanyar haurawa kan dutsen Gaoligong. Bayan an kammala hanyar mota mai sauki a shekarar 1999, ana shafe awanni bakwai ko takwas ne kafin a isa gundumar. Yanzu, bayan an bude hanyar don zirga-zirga, ana shafe awanni uku ne kawai don isa gundumar.

Xi Jinping ya ce, “Na zo ganin ku ne domin in karfafa muku gwiwa don ci gaba da yin aiki tukuru, kuma ina fatan gaya wa dukkan ‘yan kabilun da ke fadin kasarmu cewa, Jam’iyyar Kwaminis ta Sin tana kulawa da bunkasuwar dukkan kabilun kasar, ya kamata jama’ar kabilu daban daban na kasarmu su yi kokari tare don cimma nasarar kafa al’umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni.”

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da jawabi a yayin muhawarar babban taron MDD karo na 75

Wannan ganawa ta musamman ta sa kaimi ga ‘yan kabilar Dulong sosai, kuma sun kara nuna imani kan makomarsu a nan gaba.

A shekarar 2018,dukkan ‘yan kabilar Dulong sun fita daga kangin talauci.

A ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2019, Xi Jinping ya kara rubuta musu wasika, inda ya karfafa musu gwiwa cewa, “Kawar da talauci shi ne mataki na farko, kan yadda za ku kara jin dadin zaman rayuwa a nan gaba.” (Bilkisu Xin)

Exit mobile version