Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home CIWON 'YA MACE

Lafiya Jari: Alakar Cin Kwai Da Ciwon Zuciya

by Muhammad
January 22, 2021
in CIWON 'YA MACE
3 min read
Kwai
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Zanna Mustapha Wakili da Muhammad Zahraddin, 

Kwan kaji na daga cikin nau’in abinci mai inganci na yau da kullum, saboda araharsa da kuma saukin sarrafawa. Babban kwan kaza guda na da nauyin giram hamsin (50 g) ne, kuma a makare yake da furotin (6 g), kwalastaral (200 mg), daskararren mai (1.56 g), tsinkakken mai (2.76 g), nau’o’in bitamins, birbishin ma’adanai, da sauran muhimman sinadarai masu matukatar amfani ga lafiyar jiki.

samndaads

[Furotin, wato ‘protein’ kenan a turance, ajin abinci ne mai gina jiki. Kwalastaral kuwa, nau’in mai ne da ke cikin ajin kitse / mai a cikin ajujuwan abinci. Kuma bitamins na nufin ‘bitamins’ a nan.]

 

 

[Daskararren mai, wato ‘saturated fat’ a turance, nau’in mai ne da ke cikin ajin kitse / mai. Kuma shi ne irin man da ke daskarewa ko yai bacci haka kawai, misali, kakide/kitse, man shanu, manja da sauransu.]

 

Saboda yawan kwalastaral da kwai ke dauke da shi, hakan ya sa tsawon lokaci mutane ke ci gaba da kaurace wa cin kwai akai-akai, a kokarin rage yawan kwalastaral daga cimaka. Musamman, tun bayan da hukumomin kiwon lafiya suka zargi kwalastaral da haddasa ciwon zuciya kuma suka kayyade cinsa zuwa miligiram dari uku (300 mg) a kullum, kafin daga bisani hukumomin su yi watsi da kayyade kwalastaral din a shekara ta 2015. Watsi da kayyade yawan kwalastaral din da mutum ya kamata ya ci a kullum ya biyo bayan sabbin bincike da suka nuna rashin hadarin kwalastaral daga cimaka ga zuciya kamar kwai.

 

Kwalastaral muhimmin tubali ne wajen ginin bangon kwayar halitta, wato ‘cell menbrane’ a turance, baya ga kasancewarsa muhimmi wajen sarrafa wasu sinadaran jiki.

 

 

Bugu da kari, kwalastaral ya kasu gida biyu: akwai mai kyau, kuma akwai mara kyau. Kwalastaral mai kyau shi ne yake yashe ko wanke kwalastaral mara kyau daga cikin jini. Domin kwalastaral mara kyau shi ne ke kwanciya kuma ya toshe jijiyoyin jini kadan da kadan, musamman a zuciya har ya haifar da bugun zuciya.

 

Bincike daban-daban da aka gudanar sun nuna cewa babban abin da ke kawo hauhawar kwalastaral mara kyau a cikin jini shi ne daskararren mai, kamar kakide, sabanin kwalastaral da ke cikin kwai. Saboda haka, babu bukatar kaurace wa cin kwai don rage ko kayyade kwalastaral.

 

Kuma cin kwai daya ko biyu a kullum ba shi da hadarin haddasa ciwon zuciya, saboda daskararren mai da ke cikin kwai (1.56 g) kalilan ne idan aka kwatanta shi da sauran nau’o’in abinci da suke dankare da daskararren mai kamar naman shanu, madarar shanu, man shanu, cukwi/cuku, fatar kaji, askirim, da dai sauransu.

 

Haka nan, man tsirrai kamar man kwakwa, manja da man kwakwar manja na dauke da daskararren mai sosai. Har wa yau, man gyada ma na dauke da daskararren mai, sai dai yawansa bai kai na wadanda aka ambata a sama ba.

 

Daga karshe, babu damuwa ko dar-dar ga duk mai son sanya kwai cikin kunshin abincinsa na yau da kullum duba da alfanunsa ga lafiyar jiki. Saboda, i zuwa yanzu, babu cikakkiyar matsaya game da kayyade adadin kwan da mutum zai ci zuwa wani adadi, sabanin tsohuwar matsayar da ta kayyade cin kwai zuwa uku ko hudu a sati.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Charlette N’Guessan: Matashiyar Da Ta Lashe Babbar Kyautar Injiniyanci Ta Afirka

Next Post

Rashin Tattaunawa Kan Rayuwar Jima’i A Aure Matsala Ce!

RelatedPosts

Bayani A Kan Ciwon Koda Da Maganinsa

Bayani A Kan Ciwon Koda Da Maganinsa

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

koda wata halittace ta 'ya'yan ciki dake zaune kamar tagwaye...

Zuciya

Yadda Ciwon Zuciya Yake

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Zanna Mustapha Wakili da Muhammad Zahraddin, Ciwon zuciya yana...

Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe

Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe

by Sulaiman Ibrahim
4 weeks ago
0

TSAIDA BUGUN ZUCIYA:- Bugun zuciya shike gyara dumin jiki da...

Next Post
Jima'i

Rashin Tattaunawa Kan Rayuwar Jima’i A Aure Matsala Ce!

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version