Lai Mohammed Ya Bayyana Guraban Ayyukan Da Gwamnatin Buhari Ta Samar

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, a ranar Asabar din nan ne ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta samar da milyoyin ayyukan yi, ta hanyar shirye-shiryenta daban-daban a fannoni da dama.

Da yake magana a wajen yaye dalibai karo na shida na cibiyar samar da ayyuka ESI, wanda uwargidan tsohon gwamnan Jihar Ribas, Dame Judith Ameechi, ta samar. Ya ce, sama da ayyuka milyan 7 ne gwamnatin ta samar a fannin ayyukan noma kadai.

“Ma’aikatar samar da hasken lantarki, ayyuka da gidaje, ta samar da sabbin ayyukan yi har 69,736, a cikin kasarnan. Fannin samar da hasken lantarki, ya samar da ayyukan yi, 1740, fannin manyan ayyuka ya samar da ayyukan yi 38,391, sannan kuma fannin gidaje ya samar da ayyukan yi 29,605,” in ji Ministan.

Ministan kuma ya ce, shirin nan na ciyar da daliban makarantun Firamare abinci wanda a yanzun haka ya ciyar da yara milyan 6.4, a makarantu, 33,981, wadanda ke cikin Jihohin kasarnan 20, shi ma ya samar da ayyukan yi har guda, 61,352, ga madafa abinci.

Ya kuma jinjinawa, Dame Amaechi, a kan kokarin da ta yi na kafa cibiyar na ta, wacce ke koyar da sana’o’i kala-kala ga mata da matasa a yankin na Neja Delta, inda yake cewa, shigen wadannan shirye-shiryen suna tallafa wa na gwamnatin Tarayya ne, wajen samar wa da ‘yan kasa ayyukan yi.

Ya kuma umurci daliban da aka ya ye da su ci gajiyar abin da aka koya masu, wanda hakan a cewarsa, shine zai tabbatar da sakamakon da za su yi wa wadanda ke daukan nauyin horar da su.

Exit mobile version