Laifin Fyade: Ba Za A Hukunta Ronaldo Ba

Shahararren dan wasan kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, wanda a halin yanzu ya ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta Juventus wasa ba zai fuskanci shari’a ba bayan da a ka zarge shi da yi wa wata fyade a birnin Las Begas na kasar Amurka.

Kathryn Mayorga ce ta zargi dan kwallon na Juventus da yi ma ta fyade a wani otal a birnin a shekara ta  2009 sai dai tun a lokacin ‘yan sandan birnin suka bayyana cewa basu da cikakkiyar shaidar da zasu iya gurfanar da dan wasan a kotu domin a tuhume shi.

Rahotanni sun bayyana cewa Mayorga ta sasanta da shi a wajen kotu a shekara ta 2010, amma ta so ta sake shigar da kara a shekara ta 2018 shekaru goma bayan faruwar lamarin sai dai daman tun farko Ronaldo  ya musanta dukkan zarge-zargen da ta yi ma sa.

A sanarwar da su ka fitar ranar Litinin, masu gabatar da kara a birnin Las Begas sun ce sun kasa tabbatar da zarge-zargen duk da cewa Ronaldo bai musanta cewa sun hadu a Las Begas a shekara ta 2009 ba, sai dai ya ce duk abin da suka yi, sun yi ne da yardar juna.

Haka kuma ’yan sanda sunce kawo yanzu babu fefen bidiyon da za’a iya amfani dashi domin gane cewa fyade yayi mata ko kuma amincewa sukayi saboda haka basu da hurumun da zasu hukunta zaka kurin dan wasan.

Ronaldo ya koma Juventus a watan Yulin bara kuma ya lashe kyautar dan kwallon da ya fi kowa hazaka a duniya ta Ballon d’Or – a shekarun 2008 da 2013 da 2014 da 2016 da kuma  2017 tsakanin Manchester United da Real Madrid.

Exit mobile version