Abba Ibrahim Wada" />

Lakosa Ya Dawo Kano Pillars Bayan Ya Kasa Cin Jarabawa A Kasar Norway

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta bayyana cewa dan wasanta  Junior Lakosa yadawo kungiyar domin cigaba da buga wasa bayan dayaje kasar Norway domin komawa kungiyar kwallon kafa ta FC Brann ta kasar kuma bai samu nasarar lashe gwajin da kungiyar tayi masa ba.

Lakosa, wanda kawo yanzu yake da kwallaye 19 a gasar firimiyar Najeriya ya shafe makonni uku a kasar ta Norway domin gwaji a kokarinsa na ganin yakoma buga wasanninsa a nahiyar turai a kakar wasa mai zuwa.

Dan wasan, mai shekaru 27 a duniya wanda kuma tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Union Bank ne dake jihar Legas ya koma kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ne a tsakiyar kakar wasannin shekarar data gabata.

“Lakosa yadawo domin cigaba da bugawa kungiyar Kano Pillars wasa kamar yadda yasaba bayan ya je gwaji kuma bai samu ba a kasar Norway saboda haka muna masa fatan nasara kuma dafatan zai cigaba daga inda ya tsaya” in ji mai Magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Malikawa Garu.

Wannan ne dai karo na biyu da dan wasan yafita nahiyar turai domin samun kungiyar inda ko a kwanakin baya sai da yaje kasar Bulgeria domin gwaji a kungiyar Ludogorets a watan  Mayun wannan shekarar.

Tuni da dan wasan ya shiga cikin sahun ragowar ‘yan wasan kungiyar ta Kano Pillars domin cigaba da daukar horo duk da cewa har yanzu ba’a tsayar da ranar da za’a dawo gasar ta firimiya ba.

 

Exit mobile version