Maigari Abdulrahman" />

Lalacewar Hanya: Falana Ya Kai Fashola Da FRSC Kotu

Babban dan karin raji hakkin bil’adama, kuma lauya, Mista Femi Falana ya kai Ministan ayukka, wuta da gidaje, Mista Babatunde Fashola da hukumar kula da hadurra ta kasa FRSC kara a babbar kotu da ke da mazauni a Legas, bisa matsalar cinkoson manyan motoci a kan babbar hanyar Oshodi zuwa Apapa.
A cikin takardar koken karar da ya mikawa kotu, babban Lauyan na neman kotun da ta tabbatar masa da ‘yancin sa, ta kuma bawa Ministan umurni da gagagwa na janye duk wani abin ciknoso ko cikas da ke kan hanyar, tare da tabbatar da ci gaba da kula da kiyeye hanyar.
A cikin sanarwar koken da lauyan ya mika kuma, wacce ya gabatar wa mai shara’a Muslim Hassan, inda alkalin ya sanya ranar 6 ga watan Mayu a matsayin ranar yanke hukunci, ya nemi Alkalin da ya sanya dokar ajiye manyan motoci akan gada a Legas a matsayin laifi.
A cikin koken, dan karin raji hakkin bil’adaman ya rubuta cewa, ajiye motoci a kan hanyar shiga cikin hakkin sa ne da kuma ‘yancin sa na rayuwa tare da sauran matafiya da ke kan hanyar, kamar yanda sashe na 33 na tsarin dokokin Nijeriya, da kuma yanki na 4 na kundin dokokin kasashen Afurika ya tanadar.
Falana, wanda yake tsohon shugaban kwamitin masu kare hakkokan bil’adam na kasa, ya sanya karar Ministan da hukumar kiyaye hadurra ne kan yanayin da hanyar Oshodi zuwa Apapa ke ciki na rashin kyao da cinkoso.
Babban lauyan har wa yau, yana neman kotun ta hukunta cewa, rashin cire abin cinkoso da ke kan hanyar, da ci gaba da kula da ita da gyran hanyar daga bangaren wadanda yake karar, laifi ne kuma ba dai-dai ba ne tunda cinkoson barazana ne ga rayuwarsa.
Falana ya kara da cewa, rashin gyara hanyoyin take hakkinsa ne na walwala da zirga-zirga da na sauran ‘yan kasa kamar yanda yake a cikin sashe na 41 a cikin tsarin dokokin Nijeriya. Da yake kara tabbatar da abin da yake kara a kai, Lauyan ya ce, da yawan hanyoyin Nijeriya basu da kyau, ciki har da ta Apapa din.
“Na tabbatar da cewa, cinkoson ababen hawa da ke kan hanyar Oshodi zuwa Apapa baya misaltuwa, rayuwar matafiya da ke wucewa a kan hanyar cike take da hadari,” inji Lauya Falana. “sakamakon rashin kyawon hanyar, an samu hasarar rayuka da dama,” inji shi.
Falana ya ci gaba da cewa, “tafiya a hanyar ya zama abin ban tsoro da mutum bai fata ya yi. Kafin ta lalace kamar haka, a da tafiyar minti 30 ce daga Oshodi zuwa Apapa, amman yanzu ya fi awa daya.
Lauyan ya bayyan cewa, kiris ya yi saura ya yi hadari a yayin da yake kan hanyar dawowa daga ziyara a kurkukun Ikeja, lokacin da yake kokarin kaucewa wani rame, inda suka tashi karawa da wata mota da ke tafiya a dayan hannun.
To sai dai, a nasa bayanin, Minista Fashola ya musanta zargin Lauyan, yana mai cewa, ana kan gyaran hanyar ne, sannan ba hukumarsa ba ce dalilin samuar matsanancin cinkoson.
Ministan ya kara da cewa, abin da Lauyan yake kara da zargi ba gaskiya ba ne, inda ya ce, manyan motoci ne ke kawo cinkoso a hanyar ta Apapa sakamakon bin hanyar da suke yi zuwa wurin daukar kaya da sauke kaya.
Fashola ya mayar da martani da cewa, “Rashin gyaran hanyar da ma’aikatar ta ayukka ta ki yi kamar yanda wanda ke karar ke zargi, ba ta inda ya shiga hakkinsa ko ya takaita ‘yancin sa na zirga-zirga.”
Ministan ya kara da cewa, rayuwar Lauya Falana bata cikin hadari, haka kuma, matsalar rashin gyara hanyar, sakamakon rashin kudi ne, sannan, neman kotu ta masa abin da ya bukata ba dai-dai ba ne.
Ministan ya bayyana cewa, “Wanda yake karar baya da dama ko hurumin gabatar da karar, domin shi ba wakilin jama’a ba ne, kuma ma dai a madadin waye yake karar. Bai nuna wata alama ta cewa shi yafi kowa shan wahalar hanyar ko damuwa fiye da sauran mutane ba.”
A cikin takardar da mai taimakwa ma’aikatar kan harkokin shara’a ya fitar, Ayodele Otedole, Minista Fashola ya koka cewa, a irin wani koke da kungiyar direbobi ta taba shigarwa a shekarar 2010, abin ya kawo cikas da tsaikon gudanar da ayukkan hanya saboda baiwa matafiya hanya yayin da ake aiki.

Exit mobile version