Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home BULALIYA

Lalacewar Hanyoyi: A Tilasta Wa Shugabanni Tafiya A Kasa Kawai!

by Tayo Adelaja
September 22, 2017
in BULALIYA
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare da Al-Amin Ciroma            08033225331 (TES Kawai )   ciroma14@yahoo.com       

A jiya ne wani abokin aikina yake bayyana mani irin ukubar da suka sha, yayin da suka baro Legas da nufin dawowa Abuja a cikin mota. Duk da mafi yawan al’ummar Hausawa da ke Kudu suna haramar dawowa Arewa don gudun rikicin ‘yan Biyafara da ya fara kunno kai, hanyar a cunkushe take, sannan babu yadda za ka yi tafiyar kilomita daya ba a tsaya an nemi wata barauniyar hanyar da za a kaucewa wagegen rami ba.

Wannan kuwa ba wai hanyar Legas kadai ke da irin wannan matsalar ba, duk hanyar da ka dauka hankalinka zai ya tashi a kasar nan. Daga ko’ina ka fito matukar dai a kasa kake nufin bin hanya hankulan iyalai, ‘yan’uwa da abokan arziki ba ya kwanciya har sai sun sami labarin ka sauka lafiya. Idan ba a yi zancen manyan ramuka da rashin kyan hanyoyin ba, tilas a yi tunanin ‘yan fashi ko masu garkuwa da mutane. Hakan ta sa a kullum nake kara tsorata da harkokin ci gaban kasar Nijeriya.

Tambayoyi marasa amsoshi da dama sukan bijiro min a take; Anya muna muradin ci gaban kasarmu? Ko shugabanni da ‘yan siyasa su na la’akari da yadda kasashen duniya ke tafiyar da al’amuransu? Na tabbatar mahukunta Nijeriya ba za su taba bayar da amsoshin wadannan tamboyin kai-tsaye ba!

Daya daga cikin abubuwan da suka dade suna ci wa al’umma tuwo a kwarya su ne yadda shugabanni ke toshe kunnuwansu, su kuma dode idanunsu kan halin da kasar nan ke ciki ta fuskar sufuri. Duk hanyar da ka ga dama, kana iya dauka ka yi misali da shi. A wane hali hanyoyin namu suke ciki? Rayuka nawa ke salwanta a kowace rana ta Allah sakamakon lalacewar hanyoyi? ‘Yan fashi da makami na ci gaba da cin karensu ba babbaka, masu garkuwa da jama’a na yi ba ji ba babu gani. Da rana tsaka kriri-kiri, za ka iya haduwa da ‘yan fashi a ko’ina a hanyoyin kasar nan.

Bulaliyar wannan makon za ta sauka kacokan kan shugabannin kasar, musamman kan Ministan Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, kan lalacewar hanyoyin a Nijeriya. Bari mu dan yi misali da hanya Birnin Ikko (Legas) zuwa Babban birnin tarayya Abuja. Hanya ce tilo da ta hade manyan biranen kasar nan, amma abin takaici ta zama Lahirar matafiya!

Hanyar tana da fuska har guda hudu; Na farko, idan matafiya suka fito daga birnin na Ikko, za su iya bi ta Benin, zuwa Auchi, zuwa Okene zuwa Lokoja sannan su karasa Abuja. Hanya ta biyu; ana iya baro Legas zuwa Ibadan, zuwa Akure, zuwa Owo a Jihar Ondo, zuwa Ibilo, sannan a shiga Okene zuwa Lokoja, zuwa Abuja. Hanya ta uku tana tasowa daga Legas zuwa Ibadan zuwa Ilorin, zuwa Jebba, zuwa Mokwa, zuwa Bida, sannan a shiga Abuja. Sannan ta hudu ana iya barin Legas zuwa Ilesha, zuwa Esaoke a Jihar Osun, zuwa Ilaorun a Jihar Osun, zuwa Oye-Ekiti, zuwa Kabba a Jihar Kogi, a shiga Okene a Jihar Kogi, sannan a shiga Lokoja sai Abuja.

Babbar tambayar da za mu yi wa Mai Girma Minista Babatunde Fashola, shin ko ya taba tuka motarsa tun daga babban birnin tarayya -Abuja zuwa Legas? Idan har bai taba bi ba, ko ministan ya taba aika jami’ansa don gane masa halin da talakawa ke ciki da irin wahalhalun da suke sha a hanyar? Har ila yau, ko Fashola, a matsayinsa na wanda ya karbi rantsuwa da Alkur’ani cewa zaki yi wa kasa aiki, yana samun rahotannin yadda matafiya ke gamuwa da ajalinsu a kullu yaumin, ba don komai ba, sai domin tsananin lalacewar hanyar? Ko minista ya san su ma kansu jami’an ‘yan sanda sun mayar da hanyar Legas zuwa Abuja a matsayin baitul-malinsu? Ma’ana –  sun sanya shingaye da daman gaske a bisa titin, ba don komai ba, sai kawai don su rika karbar taro-sisi daga hannun direbobi mafiya? Ko ministan na ayyukan, wanda ke da alhakin gyara manyan hanyoyin kasar nan ya san cewa sakamakon yin watsi da gyaran hanyar, yanzu manyan bishiyoyi a jihohin da ke cikin Kurmi, sun kusa cinye hanyoyin kasar nan? Sa’o’i nawa ya kamata direba ya dauka daga birnin na Ikko zuwa babban birnin tarayyya – Abuja?

Kowannenmu ya san cewa nisan tafiya daga Legas zuwa Abuja bai fi kilomita 778 ba. Amma a yau, awa nawa yake daukar direba ya tuko mota ya shigo Arewa? Daga Legas zuwa birnin Badun, alal misali, direba zai ci kilomita 130 ne kacal, wato kimamin awa daya da rabi, amma sakamakon rashin kyan hanyar da cunkosun motoci, sai ya ci kusan awa uku zuwa hudu yana fafatawa. Babban abin takaici shi ne yadda aka watsar da kwangilar karasa aikin tagwayen hanyar daga Legas din zuwa birnin na Badun, shekaru da dama da suka gabata. Me ministocin baya suka yi da kudin bajet, wato kasafin da aka ware na gyaran hanyar? Haka kuma idan ka baro Ibadan zuwa Ilesha, nisan bai fi kilomita 111 ba, amma sai direba ya galabaita, kafin ya isa Jihar ta Osun. Tazarar hanyar da ta bi cikin Ilesha zuwa Owena a cikin Jihar Osun ne kadai take dan fasali mai kyau, ita ma a siyasance Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya gyara ta, a watannin karshe na gwamnatinsa don neman kuri’ar al’ummar jihar ta Osun.

Har ila yau nisan tafiya daga Akure zuwa Owo ta Ondo bai fi kilomita 130 ba, amma sai direba ya wahala yana tuki na tsawon sa’o’i biyar kafin ya isa garin na Owo. Babban tashin hankalin direbobi mabiya hanyar Legas zuwa Abuja shi ne, a daidai lokacin da suka baro Owo zuwa Lokoja, inda dududu tafiya ce ta sa’o’i biyu zuwa uku, wato kilomita 202, amma saboda takaicin halin da hanyar ke ciki, sai an dauki kimamin sa’o’i shida zuwa bakwai! Azabar da matafiya suke fuskanta a wannnan hanyar ba ya misaltuwa, asarar rayuka da dukiya sai dai a yi shiru, amma duk da haka, shugabanni da ministocinsu gami da manyan ‘yan siyasa, suna ci gaba da tallata hajojinsu na ci gaba, babu ruwansu da halin da al’umma ke fada ciki!

Bari mu kalli wasu kasashen duniya da suka yi mana fintinkau a harkar kula da talakawansu ta fuskar sufuri. Faransa alal misali, nisan tafiya daga garin Lyon zuwa Gueret shi ne kilomita 324, haka ma nisan tafiya a mota daga birnin Berlin zuwa Wettinberg a kasar Jamus kilomita 110 ne. Daga birnin Oklahoma zuwa Dalas na kasar Amurka kuwa, kilomita 305 ne. Amma za ka iya zuwa sau goma a yini daya ba ka galabaita ba. Ko’ina a gyare yake, babu cinkoson motoci na fitar hankali, jami’an tsaro ba sa musguna wa direbobi a kan hanaya. Baki daya kasashen nan da muka lissafa, ba su fi Nijeriya da komai ba. Kai, hatta kasashenmu na Afrika, idan muka dauki kasar Kamaru, daga birnin Younde zuwa Douala, kilomita 230 ne, amma ji za ka yi kamar daga Zariya zuwa Kaduna ne, sabili da tsarin titunansu, komai lafiya lau, idan dare ya yi, ko’ina a haske da fitilu.

Me muka rasa a Nijeriya? Me ya sa jami’an gwamanti ba su dauki rayuwar talaka a bakin komai ba? Ina amfanin bajet din da ake tayar da jijiyoyin wuya a kai? Ko don saboda su da iyalansu da mukarrbansu ba sa bin hanyoyin ne? Tilas ne a hana shugabanni hawa jiragen sama a cikin gida, su rika bin tituna, ko ba komai za su ji a jikinsu.

Amma abin da ya kamata Ministan Ayyuka Babatunde Fashola ya sani shi ne alhakin rayukan talakawa da ke salwanta a kullu yaumin su na wuyansa. Wani babban albishir a gare shi kuwa shi ne, ya zuwa yanzu ya cinye kwanaki 846, a cikin kwanaki 1461 din da zai yi a gadon mulki, wato shekara hudu. Yanzu saura kwanaki 613 kacal suka rage masa!

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Al-Bashir Ya Bukaci Komawar Wadanda Suka Tsere Daga Darfur

Next Post

BABBA DA JAKA

RelatedPosts

MUKALAR LITININ: Guguwar ’Yan A Kwafe – A Watsa A Yanar Gizo ‘Copy and Paste’

MUKALAR LITININ: Guguwar ’Yan A Kwafe – A Watsa A Yanar Gizo ‘Copy and Paste’

by Tayo Adelaja
3 years ago
0

A wannan makon ina so ne na yi tsokaci dangane...

Tunaninka Kamaninka: Yaushe Za Ka Zama Attajiri?

by Tayo Adelaja
3 years ago
0

Al-Amin Ciroma 08033225331 (TES Kawai )   ciroma14@yahoo.com       Ina yi wa...

Badaƙalar Maina: Tsakanin Dambazau Da Oyo-Ita, Wane Ne Mai Gaskiya?

by Tayo Adelaja
3 years ago
0

Al-Amin Ciroma  08033225331 (TES Kawai )   ciroma14@yahoo.com        Zancen da ya...

Next Post

BABBA DA JAKA

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version