Zubairu T M Lawal" />

Lalacewar Ilimi: Ajujuwan Karatu Na Barazana Ga Rayukan Dalibai A Nasarawa

Dubban dalibai na kaucewa shiga ajujuwan karatu sakamakon gujewa barazanar rayuka saboda lalacewar ajujuwa.

Mafi yawan ajujuwan karatu sun zamo abin tsoro a makarantun Gwamnatin jihar Nasarawa. Makarantun Firamare na yara kanana ba su tsira daga wannan ambaliyar lalacewar ajujuwan ba.

Wasu makarantun yara kanana ba su iya shiga ajujuwa saboda lalacewar ta wuce misali. Sai dai su zauna a gindin bishiya ko kuma a harabar makaranta.

Babban abin tsoro shi ne zafin rana yakan addabi kananan yara da ke karatu a cikin dakunan da babu rufin kwano. Haka-zalika da zarar ana ruwan sama malamai kan kwashe yara su kai su wasu guraren su fakewa ruwan sama.

Idan kuma aka yi ruwan sama na dare to yara ba su iya shiga aji da safe saboda ruwa na kwanciya a cikin ajujuwan.

Makarantu da dama suna fuskantar wannan matsalolin, kuma an kasa gyarawa duk da cewa hukumar ilimin bai-daya ta jihar Nasarawa, UBE tana ikirarin cewa tana kashe milyoyin kudi wajen gyaran makarantu musamman na Firamare, amma ayyukan da idanuwan jama’a ba su gani ba.

A kwanaki wakilinmu ya ziyarci wata makarantar Sakandire da ke cikin birnin Lafiya mai suna, GSS Isyaka. inda ya ganewa idanunsa yadda yara ke zama cikin hadari.

Sakamakon duk ajujuwan da ‘yan Sakandire ke karatu abin tsoro ne. Saboda dakunan karatun sun lalace rufin saman kwanon sun lalace, wasu ajujuwan ma idan ana ruwan sama sai dai dalibai su tsaya a tsaye cikin takura suna kaucewa ruwan saman.

Sannan ga silin na rufin ajujuwan yara da sun mike tsaye hannuwansu na taba silin din.

Wasu ma kamawa suke yi suna lilo. Makarantar babu isassun ajujuwan karatu, wannan wadanda ake da su babu kyau suna barazana ga rayukan dalibai.

Rashin isassun ajujuwan ya sanya aka raba dalibai wasu na zuwa da safe wasu da rana.

Haka-zalika, makarantar Sakandire ta GSS Maina, wacce ita ma tsohuwar makaranta ce a garin Lafiya, duk da cewa tsohuwar Gwamnatin da ta shude ta kashe milyoyin kudi wajen yin kwaskwarima inda ta gina Katanga ta gewaye makarantar amma ajujuwan da ke makarantar ko akuyoyi ba za a bari su kwana a cikin su ba, saboda barazanar ruftawa.

Yanzu haka ita ma makarantar ta GSS Maina tana bukatar agaji daga Gwamnati.

Makarantar Mada Station da ke yankin karamar hukumar Nasarawan Eggon, tana cikin jerin Makarantun da idan ba a kai masu agaji ba to zuwa wani lokaci makarantar za ta zama tarihi ko ta bar mumunan tarihi na asarar rayuka. Saboda  Gwamnati ta kware rufin da sunan za ta gyara  amma shuru kake ji.

Ya zuwa yanzun gara dalibai su zauna a waje a filin  kwallo su yi karatu da a ce suna zune cikin ajujuwan. Haka Makarantar Sakandire ta Tudun Amba, da ke garin Lafiya ita ma wannan matsalar take fuskanta.

Haka ma wasu makarantu da ke fadin jihar Nasarawa suna fuskantar matsalolin lalacewar ajujuwan karatu.

Exit mobile version