Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa lalacewar tsarin zabe babbar barazana ce ga dorewar dimokuradiyya a Nahiyar Afirka.
Tsohon shugaban kasa ya ce sai masu ruwa da tsaki sun hada kai wajen sauya tsarin zabe, in ba haka ba tsarin dimokuradiyya na iya rushewa a wannan yanki.
- Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
- A Karo Na Hudu ’Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Sun Yi Nasarar Kammala Ayyukansu A Wajen Kumbon
Jonathan ya bayyana hakan ne a lokacin taron tattaunawa kan dimokuradiyya da gidauniyar Goodluck Jonathan ta shirya a Accra, babban birnin kasar Ghana, tsohon shugaban kasa ya bukaci shugabannin siyasa su yi kokarin sanya dimokuradiyya ta tabbatar da kyakkyawan makoma ga matasa masu tasowa, wanda muryoyinsu ke da muhimmanci.
Rahotannin dai sun bayyana cewa jam’iyyar PDP na tunanin bai wa Jonathan tikitin takarar shuugaban kasa a zaben 2027.
Jonathan ya karbi shugabancin Nijeriya a shekarar 2010, bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua. Ya yi takara a zaben shugaban kasa na 2011 karkashin jam’iyyar PDP kuma ya samu nasara.
Haka kuma, ya fadi zaben shugaban kasa na 2015 ga dan takarar jam’iyyar APC, Marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a watan Yuli na wannan shekara.
Akwai zazzafar muhawara kan dokar da ta bai wa Jonathan damar sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma daya daga cikin shahararrun jiga-jigan jam’iyyar PDP, Sule Lamido, a kwanan nan ya bayyana Jonathan a matsayin mafi kyawun dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2027.
Lamido ya kuma yi kira da shugabancin jam’iyyar na kasa su yi kokarin tabbatar da an tsayar da shi takarar shugaban kasa a 2027.
Jonathan ya ce, “Dimokuradiyya a Nahiyar Afirka na fuskantar babbar barazana, sannan ta kusa da rushewa sai dai masu ruwa da tsaki sun hada kai kafin su iya ceton ta daga wannan babbar barazana. Lalata tsarin zabe na ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan barazanar da ke cikin Afirka.
“Mu a Afirka dole ne mu fara duba dimokuradiyyarmu da kuma sake tunani kan hanyar da za ta yi mana aiki da kyau da mutanenmu. Daya daga cikin manyan matsalolin shi ne, tsarin zabenmu. Mutane suna amfani da hanyoyin damfara don ci gaba da kasancewa a mulki ta kowanne hanya.
“Idan muna iya gudanar da sahihin zabe, duk shugaba da ya gaza yin aiki za a kayar da shi daga kan mulki. Amma a cikin al’amuranmu, mutane suna amfani da tsarin zabe domin su ci gaba da zama a kan kujerar mulki duk da cewa mutane ba sa son su.
“Mutanenmu na son samun ‘yancinsu. Suna son kuri’unsu su yi tasiri a lokacin zabe. Suna son wakilci bisa adalci da samun hadin kai.
“Suna son ingantaccen ilimi. Mutanenmu suna son tsaro da samun ingantaccen kiwon lafiya. Suna son a ba su aikin yi. Suna son a ba su daraja. Lokacin da shugabanni suka kasa cika wadannan bukatun, mutane ba sa son haka,” in ji Jonathan.