Connect with us

MAHANGA

Lalata Da Dalibai A Jami’o’in Kasar nan (1)

Published

on

Ga duk mai bibiyar al’amuran da suka shafi shafin yanar gizo, ko kuma in ce harkar yada labarai a kasar nan ya san yadda a ‘’yan watannin nan ake yawan samun koke-koken game da yadda wani Malaman Jami’o’I ko lalata da dalibansu dom a bas u maki, ko kuma don a kais u inda bas u kai ba a harkar jarabawa.

Ko ba a ce komai ba, wannan wani mummuna  abu ne da za a iya cewa bai kama da hakali ba, ko kuma mu ce wani abu ne da za ma bala’in da in ba hankali aka yi ba zai iya zama wata annoba da za ta taba tarbiyyar rayanmu da kuma kawo mummunan nakasu a harkar ili a kasar nan.

Irin wannan abu da wadannan bata-garin Malamai suke yi, wani abu ne da aka jima ana yinsa, sai dai bai zama ruwan dare ba kamar a ‘’yan watannin nan, inda ake kamawa, tare da daukan mataki a wani makarantun. Amma wasu kam har yanzu suna nan suna cin karensu babu babbaka.

Sai dai duk da haka za a iya cewa ana samun sauki, domin an saba idan irin wadannan abubuwa suna faruwa ba a daukar wani mataki a kai, bilhasali ma idan wata daliba ta kuskura ta kai karar irin wannan cin zarafi, to kashinta ya bushe, domin Malaman za su hade mata kai ne, su gaba gaba har wajen Hukumar makarantar su karyata ta, a karshe a ce it ace ba ta gaskiya.

To amma a ‘’yan watannin nan abin ya zama bah aka ba, domin duk yarinyar da ta kai irin wannan kara, to Hukumar makarantar tana daukar matakin da ya dace wajen hukunta irin wadannan mugayen Malaman.

Akwai musalai da dama inda aka dauki irin wannan mataki. Misali, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, an kama wani Malamin wanda yay i fice a irin wannan aika-aikar, inda kuma bayan bincike ta hanyar wani kakkarfan kwamiti, aka sallame shi.

Amma sai dai abin takaici, bayan ‘’yan watanni sai aka yi wannan Malami ya samu aiki a Jami’ar jihar Kaduna. Kodayake nag a an sanya batun a gaba a yanar ginzo, inda har na ba cin karo da wani martini na Gwamna Malam Nasir El-rufai, inda yin godiya game da wannan nusarwa da aka yi masu, kuma y ace Kwamishina Ilimi da Kwamishinan shari’a za su bi lamarin.

Haka kuma a jihar Ekiti, Hukumar gudanarwar Jami’ar jihar ta kori wani Malamin Jami’ar mai suna Olola Aduwo, korar kuma irin korar da Marigayi Musa Dankwaro ke fadi, ‘Ba Fansho Ba Garatuti.’ Korar da ta fara aiki daga watan Oktobar da ya gaba sakamakon kama dumu-dumu a irin wannan badala.

Irin wadannan misalai suna da yawa, wadanda kuma na tabbata ana daukansu ne don ya zama sarasi ga wasu, duk da yake wasu dai abin ya zama masu jiki, amma dai idan kore na yawo, sanda na yawo, wata rana za a hadu.

Kamar yadda na fada a sama, abin farin cikin shi ne yadda Hukumomi a Jami’o’i da gwamnatoci ke daukar abin da muhimman a yanzu fiye da a da, wanda daliba ba ta da wani abin yi, ko dai ta ba da kai bori yah au ko kuma ta rasa karatun.

Wani abin farin ciki shi ne a kwanakin baya Majalisar Dattawan kasar nan ta gabatar da wani kuduri mai zafin gaske da zai dakile yawaitar irin wannan cin zarafin da key i wa mata a Jami’o’i.

Wannan dokar da za ta taimaka wajen dakile yawaitar wannan cin zarafin mata ta nau’o’i daban-daban, walau ko ta tursasa musu a yi zina da su don a ba su maki, ko karbar kudadensu, ko wasu hanyoyi, idan an samu nasarar dokar, za ta taimaka wajen wa dalibai a manyan makarantun da suke kasar nan.

Wannan dokar tana zuwa ne a daidai lokacin da korafe-korafe ya yi yawa game da wannan lamari, wanda kuma kowa na ammannar cewa idan har aka tabbatar da ita, to za ta taimakawa ‘’ya’’yan jama’a.

A cikin tanadin wannan doka da Majalisar ta gabatar, an ware wa’adin shekaru har 14 a kurkuku ga duk Malamin da aka cafke yana lalata da wata daliba a duk fadin kasar nan, ba tare da wani zabi na biyu ba.

Kudurin wanda ya zarce karatu na daya da na biyu a Majalisar Dattawan, Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Obie-Omo Agege ne ya gabatar da shi, da fatan idan ya zama doka zai kawo karshen wannan cin zarafin.

Akwai bayanai da dama da muke son yi a wannan maudu’i, kama daga jin ta bakin wasu daliban da kuma wasu iyayen da dai sauran bayanai.

Haka kuma ga duk mai son tofa albarkacin bakinsa, zai iya aikowa ta leadershipayaulahadi@gmail.com ko mahawayi2013@gmail.com.
Advertisement

labarai