Connect with us

MAHANGA

Lalata Da Dalibai A Jami’o’in Kasar nan II

Published

on

Mai karatu barkanmu da sake saduwa a wannan fili namu na Mahanga, inda muke yin bayanai game da abubuwan da suka shafi yau da kullum, wadanda Allah cikin ikonsa ya ba mu ikon hangowa, kuma muka ga ya kamata mu dan wayar da kan jama’a a ciki, ko kuma mu yi tsokaci don wadanda abin ya shafa su Ankara.

In dai ana biye da mu, a makon da ya gabata mun fara bayani ne game da mummuna bala’in nan da ake fama da shi a manyan makarantun kasar nan, inda ake samun Malamai suna lalata da ’ya’yan mutane don kawai su ba su maki, ko kuma don kar su kayar da su a jarabawa.

Wannann wani bala’i ne da yake tashe a yanzu a kusan duk wadannan Jami’o’i da sauran manayan makarantun gaba da Sakandare da ke kasar nan, sai dai idan abin bai bayyana ba, amma abin ya zama ruwan dare.

A makon da ya gabata mun ce za mu ci gaba da bayyana ra’ayoyin jama’a game da wadannan abubuwa, inda muka fara kawo maku wasu, a yau kuma za mu ci gaba cikin yardar Allah.

Wata daliba daga Jami’ar ABU da ke Zariya, wacce kuma ta nemi a sakaye sunanta don wasu dalilai, wacce kuma ta ke matakin karatu na biyu, ta bayyana cewa suna cikin tsaka-mai wiya a duk lokacin da suka ga wani Malami na neman wata alaka ta hada su.

“Gaskiya ko ni wani Malami ya yi kokarin jan ra’ayina kan wannan badala, duk da na yi kokarin fin karfin zuciyata, sai Allah ya taimakeni a kai, na samu waraka a sakamakon wasu matakai da na dauka cikin hikima da suka hada da daure wa Malamin fuska a duk lokacin da yake magana da ni, sai bai samu fuskar da zai sake nemana da wani abu marar kyau ba,” in ji ta.

Ta ci gaba da bayyana cewa, “amma matsalar ita ce, wani lokacin gaskiya ana fin karfin imanin dalibai mata ake yi, har a kai ga yin fitsara da su; misali, wasu daliban za ka tarar suna fadawa cikin tsananin bukata, walau ta rayuwa ko ta wani abin da dole sai sun nemi agaji, hakan ya fi faruwa da daliban da suke makarantar kwana, a irin wannan gabar ne ake samun nasara har a yi galaba a kan wasu daliban mata.”

“Amma a wannan bigiren, ina baiwa ‘yan uwana dalibai mata shawara da cewar duk halin da ki ka tsinci kanki, walau na karewar kayan abinci ne, ko kudin tafiyar da wasu abubuwan neman ilimi, to lallai ki daure ki yi hakuri Allah zai kawo miki mafita, ba biye wa son rai wajen yin fasadi ba,” A cewar ta.

Shi kuwa wani babban Malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke Bauchi, Malam Hassan Hassan ya bayyana ra’ayinsa ne kan wannan batun da cewa; “A tunanina, ba rashin dokoki ne matsalarmu a kasar nan ba; akwai dokoki da dama, to amma ba ma amfani da su. Ma’ana, ba ma aiwatar da hukuncinsu. Sannan ga gazawar kotuna da fasadin Alkalai.

Ya ci gaba da yin kira da cewa, “sannan kuma mu nemi gwamnatocin jihohi su aiwatar da dokar kula da yara ta 2013. Akwai sassa a cikinta wanda suke sa iyaye da Malamai da makarantu da kowa ya tashi akan himmarsa akan yara da aka ba su amana, idan kowa ya yi haka, to dukan matsalolin za su ragu ainun, ko ma su kare.”

Shi kuwa Malamin Jami’a cewa ya yi illar yi wa dalibai fyade a manyan makarantu matsala ce babba wacce ta ke bukatar hada karfi da karfe daga kowace bangare domin dakile matsalar, inda ya yi nuni da cewa sanya doka mai tsauri ne kawai zai kawo raguwar matsalar.

Ya ce, “a gaskiya wannan kuduri na Majalisar Dattawa, ya zo akan gaba, domin in ka lura yawaitar lalata da ‘ya’ya mata dalibai ya yi yawa a Jami’o’in Nijeriya, kuma in har ba an samu doka mai tsauri akan yin hakan ba, to hakika ba za a taba shawo kan wannan matsala ba.

Duk kuwa da cewa, wasu suna ganin matsalolin ba daga Malaman ne kawai ba. Misali, su ma yaran in aka yi rashin sa’a ba su samu tarbiyya mai kyau ba daga gidajensu, suna iya neman a yi lalata da su don bukatarsu ta kashin kansu, walau ko don neman maki a bisa gandar karatu ko kuma don neman wani abu na duniya.

To, amma dai yin dokar zai taimaka kwarai wajen rage irin wannan aika-aikar, domin duk wanda ya san in an kama shi za a yi masa hukunci mai tsanani, to lallai ba zai taba yarda ya
Advertisement

labarai