Abubakar M Tahir">

Lamarin Ambaliya A Kasar Hadejia Kaddarace Daga Allah—Inji Malam Salisu Birniwa

Mai Karatu wannnan tattaunawace da wakilinmu Abubakar M. Taheer ya yi da Malam Salisu Muhammad Birniwa Sakatare na kungiyar Hadejia Ina mafita kan ambaliyar ruwa data faru a yankin. Wanda suna cikin kungiyoyin da suka tsaya kai da fata wajen yin jinga.Da kuma taimakon mutane da de saura batutuwa asha Karatu Lafiya.
Zamu so ka gabatar dama da kanka ga masu Karatu.
Sunana Salisu Muhammad Birniwa nine sakatare na kungiyar cigaban masarautar. Hadejia ta Hadejia Ina Mafita Initiatibe.
Mene makasudin ita wannan amabaliya data faru
Kamar yadda muka Sani ita ambaliya Allah ne yake kawota ta sanadin Ruwan sama da kuma Ruwa kogi. Wanda dama a addini mun San akwai kaddara.
Ya zuwa yanzu an iya Sani irin asarar da aka samu a kan wannan lamarin.
Lalle duk wanda yace ya kididdige iya ta’adin da ruwan yayi zai fadi iya abinda ya sani ne tunda har yanzu nan bai dena ta’adin ba.amma akwai Wanda suke da hakkin kiddigar tinin sun fara gudanar da aikinsu.
Mutane sun tsaya kai da wata wajen taimakawa ta naku janibin ya abin yake
Alhamdulillahi mutane sun taimaka kwarai da gaske na farko rukunin matasa Wanda suke aiki ba dare ba rana wajen jinga sun taimaka gaya.yara da many a sun fito harda mata sun fito wasu sun taimaka da karfinsu wasu tunaninsu wasu da dukiyoyinsu har Allah ya tsayar mana da al’amarin.
Ta janibin Gwamnati wani taimako aka samu
Ba zan iya ambata abinda sukayi gaba daya ba.Amma na farko tun taletale sun yi ta bada shawara kan guraren daya dace ayi aiki da kuma Inda yake da matsala.wanda suke hanyar Ruwa.
sannan kuma Gwamnatin Jihar Jigawa data Tarayya ta kafa kwamitin wanda suk zo suka duba Amma gaskiya sunyi kokari sosai.
Ta janibin Alummar gari fa
Lalle mutane sun taimaka musamman wanda abin ya shafa na kauyuka sun mutanen gari sun basu gidaje su sun zauna wanda daga baya wasu suka koma makarantu domin samun tallafin Gwamnati.wasu ambasu katifu da gidan saura.
Sannan kuma manya mutane irinsu magayaki da gidan galadiman kalgwai da sauransu suma sun tattafa saide Allah ya saka musu da alkairi.
Wace shawara kuka bama Gwamnati ta Janibin kungiyarku
Lalle mun basu shawara akan shirin gyaran kogi tunda kusan dama matsalar idan an sako ruwan Dam ne ake samun matsala to asaki ruwan kogin inyaso masu aikin rani suyi daga baya idan damana tayi sai ruwan yayi balancing kaga muna tunanin baza’a samu aukuwar lamarinba.
Wani kira kuke dashi ga Alummar kasar Hadejia baki daya
To sako na farko shi ne kowa ya sani wannan Lamarin Allah ne ya kawoshi kuma mu Sani jarabace Daga Allah Ba kowane ya kawoshiba Mutum ya yi kadan ya haifar da hakan, wani abin ma halinmune yake jawo mana a jarabcemu. Kamar yadda ya bayyana a cikin littafinsa mai tsarki.
Abu na gaba shi ne a cigaba da addua kan kada Allah ya sake kawo mana irin wannan lamarin.Sannan kuma Ina fatan Allah ya maidawa wanda suka rasa dukiyoyinsu da alkairi. Ya maido musu da sabon arziki.
Sannan ina kira ga wanda ruwan yayima ta’adi shine su duba wane amfanine zasu saka bayan ruwan ya tafi kada su zuba ido su kasa amfanar wani Abu misali alkama,Masara da sauransu.

Exit mobile version