Wani Lauya mazaunin garin Abuja Mista Pelumi Olajengbesi ya yi suka akan tsarin shekaru na daukar aiki da kamfanin NNPC yake hakin y a yanzui.
A cikin wasikar da Lauyan ya aikawa Babban Manajin Darakta na rukunonin kamfanin na NNPC Dakta Maikanti Baru a ranar 26 ga watkn Maris Olajengbesi ya yi barazanar maka kamfanin a gaban kuliya saboda nuna ban-bancin shekaru wajen daukar aikin bayan da kanfanin ya sanar da daukar sababbin ma’akata.
A ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2018 kamfanin na NNPC ya bayar da tallan sanar da daukar sababbin ma’aikatan wadanda shekarun basu wuce shekaru 28 kuma dole wadanda za’a daukar su kasance jama’a suka kammala ko kwalejin fasaha da kumiyya kafin shekarar 2014.
Olajengbesi ya nuna jayayyar sa akan cewar, yin amfani da shekarun sun sabawa sashi na 3 (e) da (ib) a cikin baka na dokar yancin ykn adam ta shekarar 2009 data baiwa yan Njijeriya kariya akan ra’ayoyin su.
Ya ci gaba da cewa, bayan tallar da aka buga ta daukar aikin na shekarar 2019, kamfanin na NNPC ta nuna cewar, sai wanda suka kammala jami’a za’a dauka aikin a kamfanin kuma dole wadanda za’a dauka aikin, shekarun su kai samada 28, 34 da 37, inda ya yi nuni da cewa, wannan nuna wariya ce kawai ga yan Niheriya.
Acewar sa, “ina son in nuna jayayya ta akan hakan karara akan wannan tsarin na daukar sababbin ma’aikatan da ake kan ci gaba da yi, inda ya kara da cewa wannan matakin wani salo ne na dannewa sauran yan Niheriya da suka chanchanta kamfanin ya dauke su aiki.
Ya kara da cewa, ya nuna jayayyar sa akan s’tsarin na daukar aikin ne akan hujjar sashe na 42 na kundin tsarin mulkin Nijeriya da aka sabunta na shekarar 1999 wanda ta hana nunawa dukkan yan Niheriya wariya.
Acewar sa, kamfanin NNPC a matsayin sa na gwamnatin tarayya dole ne ya baiwa dukkan yan Nijeriya hakkin su kuma abin takaidi ne akan yadda kamfanin yake nuna wariya da kuma yiwa kundin tsarin mulkin Nijeriya karan tsaye.
Sai dai, a cikin sanarwar da Janar Manaja na sashen hudda da jama’a Mista Ndu Ughamadu ya fitar a ranar Larabar data gabata a garin Abuja, kamfanin ya yi ikirarin cewar, yana da ikon yin amfani da tsarinbda yake so na daukar sababbin ma’aikata.
Ughamadu ya ce, daukar aikin kashi na farko an kammala shi kuma za’a yiwa wadanda aka tantance yiwa gwaji a cibiyoyi 50 dake daukacin fadin kasar nan.
Ya kara da cewa, jashi na farkon an buga a wasu jaridun kasar nan da kuma wasu kafafen yada labarai na yanar gizo a ranar 13ga watan Maris an kuma kammala a ranar Talata.
A karshe Ughamadu ya ce, kashi na biyu kuma ya hada da daukar sunayen wadanda suka ci nasara kuma za’a gayyato su don ayi masu gwaji ta hanyar yin amfani da kwamfuta kuma za’a yi gwajin ne a cibiyoyi 50 dake daukadin fadin Nijeriya.