Connect with us

LABARAI

Lauyoyi A Jihar Ribas Sun Yi Zanga-zanga A Kan Karancin Albashi

Published

on

Daruruar lauyoyi ne a jihar Kross Ribas a karkashin hadaddiyar kungiyar lauyoyi na “Law Officers Association of Nigeria (LOAN)” suka gudanar da wani zanga zanga na yin tir da karancin albashin da ake basu da kuma tashin kyautata musu a yayin gudanar da aiyyukansu.

Lauyoyin sun yi tir da halayyar Ministan shari’a na jihar, Joe Abang, a kokarin da yake yin a kawo cikas don kawo karshen matsalar da kuma jinkirin samar da hadadiyar tsarin albashi tsakanin masu shari’a da kuma lauyoyi na jihar.

Lauyoyin sun sha alwashin cewa, babu wani lauya da zai koma bakin aiki a ma’akatar shari’a har sai an biya musu bukarunsu.

“Muna zanga zanga ne don neman biyan bukatunmu, muna da hujjojin wannan gangami namu, tsari ne na dokokin gwamnati na samar da banbanci tsakanin albashin masu shari’a da kuma lauyoyi.

“Kwanaki da gwamna ya zo kaddamar da dakin karatu a ma’aikatar shari’a ya yi alkakwarin samar da hadadiyya tsarin albashi da kuma alkawarin daukan karin lauyoyi, to lalai an dauki karin lauyoyi amma har yanzu ba a samar da tsarin albashin da muke magana ba,” inji su.

A nasa tsokacin a cikin sanarwa daya rabawa mane ma labarai, Abang ya ce, a halin yanzu al’amarin sabon tsarin albashin lauyoyin na a gaban shugaban ma’aikata, Barr Ekpenyong Henshaw da kuma ofishin A kanta janar na jihar, ya kuma yi gargadin cewa, gwamnati ba zata yi jinkirin aiwatar da dokan kin biyan albashi in har ba a yi aiki ba, “no work, no pay policy.”

Mukaddashin Gwamnan jihar, Farfesa Ibara Esu, ya bukaci lauyoyin su koma baki aikinsu yana mai alkakarin yin kyakyawan nazarin matsalar da nufin biya musu bukatunsu.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: