Daga Idris Aliyu Daudawa
A ranar Talata wasu lauyoyi da masu shigar da kara a Kaduna suka bayyana ra’ayoyi mabambanta game da yajin aikin da kungiyar ma’aikatan shari’a ta Nijeriya (JUSUN) take yi wanda ya kai ga rufe kotuna a duk fadin Nijeriya.
Mafi yawan lauyoyin da manema labarai suka zanta da su sun nuna goyon bayansu game da shi yajin aikin, inda wasu kalilan ne ke cewa matakin zai haifar da rugujewar tsarin shari’ar kasar.
Wani lauya mai suna Dabid James, wanda ya nuna adawa da yajin aikin ya yi ikirarin cewa hakan na iya kawo durkushewar tsarin adalci a Nijeriya.
A cewar James, yajin aikin zai hana wadanda ke jiran shari’a saurin yanke masu hukunci game da shari’unsu, yayin da kuma, wasu za a sanya lauyoyi rashin aiki, ta hakan ne zai iya shafar kudaden shigar su.
Ya ci gaba da bayanin cewa aikin kunghiyar ma’aikatan kotuna wato JUSUN ke yi na iya kara yawan talauci da aikata laifuka, idan ba a warware shi al’amarin a kan lokaci ba.
“Matakin da aka dauka kamar yadda ya ce, ya keta hakkokin bil adama na fursunoni kuma hakan zai sa ba za a bayar da belin wadanda ake zargi ba, a irin wannan misali, fursunoni ne ke shan wahala saboda yajin aikin, kasancewar shari’arsu na ci gaba da jinkirtawa a kotuna .
“Misali, wasu daga cikin wadanda nake karewa ana tsare da su ba bisa ka’ida ba ake tsare su da ‘yan sanda ke yi, saboda ba a gurfanar da su a gaban kotu ba dalilin shi yajin aikin,” in ji shi.
Don haka ne ya bukaci gwamnati da ta saurari bukatun kungiyar JUSUN, idan har yin hakan zai kawo gyara a tsarin shari’a.
Shui kuwa Karim Abdullahi, wani lauya da ke nuna goyon bayan sa akan JUSUN, ya bayyana cewa ba daidai ba ne idan gwamnati ba ta damu da abubuwan da ke faruwa a bangaren Shari’a ba.
Ya shawarci gwamnati da kungiyar kwadagon da su warware matsalolin cikin gaggawa.
Wadanda ya kamata a tattauna dasu ya kamata a tattauna dasu, kuma a lokacin da aka dauki shi matakin, ana iya aiwatar da hakan, za’a yi sulhu, ba za a sami mai nasara ba, babu kuma wanda zai yi hasara.
Abdullahi shi kuma ya kara da cewa “JUSUN ba za ta iya samun duk abubuwan da take so ba, kuma gwamnati ba za ta iya dunkule hannayenta ta ga ba ta damu ba, bare su zauna su yi yarjejeniya, a kan muhimman abubuwan da ke tabbatar da cewa ma’aikatan kotuna sun janye yajin aiki.”
Sai dai kuma ya lura da cewa yajin aikin zai shafi fursunoni da suke fuskantar shari’ar aikata laifuka na tsawon shekaru biyar zuwa shida.
Abdullahi ya yi kira da gwamnati da ta mika wuya ga bukatun ma’aikatan bangaren shari’a saboda abu ne da ya dace kuma a yi adalci ga wadanda ke jiran shari’a.
Hakanan, Paul Daniel, ya ce zai yi kyau idan aka amince da bukatun JUSUN kan cin gashin kai, tunda bangaren shari’a wani bangare ne na gwamnati.
A cewarsa, ma’aikatan shari’ar suna yaki ne da kyakkyawar manufa, duk da cewar yajin aikin tabbas zai ci shi da abokan huldar sa na aiki masu yawa.
“Ina goyon bayan ikon cin gashin kai na bangaren shari’a don duba yadda ya kamata a cikin gwamnati.
Daniel ya ce “Idan har bangaren shari’a dole ne ya kasance ba ya nuna son kai, to ‘yancin cin gashin kai, ko ikon cin gashin kansa wani al’amari ne da ba za a iya dadewa ba.”
Hakanan ma wata mai shigar da kara, Rukayya Adamu, ta nuna bakin ciki game da yajin aikin tare da bayyana fatan za a kawo karshen shi nan ba da jimawa ba.
Adamu, wanda aka gabatar da karar sa ta farar hula, ya ce abin takaici ne yadda kotunan suka kasance a rufe saboda yajin aikin.
Wani mai shigar da kara, Aliyu Ibrahim, ya ce ya bar gida da wuri domin ya bayyana a gaban kotun, amma ya ji takaicin haduwa da kotun a rufe.
Ya kuma yi kira da a hanzarta warware su matsalolin, “don talaka ya samu damar samun adalci.”
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya bada rahoton cewa shugabanin JUSUN na kasa a cikin wata yarjejeniyar da aka cimmawa, ta ranar 1 ga Afrilu, sun ba da umarnin rufe kotuna a duk fadin tun daga ranar 6 ga Afrilu.
Shi wannan umurnin ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 21 da gwamnatin ta bayar don aiwatar da cikakken ikon cin gashin kan bangaren na shari’