Khalid Idris Doya" />

Lauyoyi Sun Bai Wa Gwamnatin Bauchi Tallafin N500,000 Don Yaki Da Korona

Lauyoyi da ke Bauchi a karkashin kungiyarsu ta ‘Body of Bauchi Lawyers of Conscience’ (BOBALAC) tare da kungiyar ‘Bauchi Assembly of Youths Actors’ (BAYOPA) sun baiwa gwamnatin jihar Bauchi tallafin kudade da yawansu ya kai naira dubu dari biyar domin yaki annobar Koronabairus a jihar.

Shugaban kungiyar BOBALAC, Jibrin S. Jibrin Esk, shine ya shaida hakan a lokacin da suka kai ziyara wa kwamitin dakile yaduwar cutar na jihar a gidan gwamnatin Bauchi a makon da ta gabata.

Jibrin S. Jibrin ya kara da cewa tallafin na daga cikin kokarinsu na ganin an hada kaifi da karfe wuri guda domin yakar cutar da ke illa wa tattalin arzikin jihar.

“Hadakarmu BOBALAC da BAYOPA mun zo ne domin mu taimaka wajen yaki da cutar ta fuskacin bayar da tallafin kayyaki da kudade hakan na cikin bangaren taimakon al’umma da ke kanmu.”

Shugaban ya bukaci gwamnatin tarayya tare da masu ruwa da tsaki, kamfanoni da daidaikun jama’a da su taimaka wa gwamnatin jihar domin tabbatar da yakar cutar.

Mataimakin gwamnan jihar wanda shine shugaban kwamitin dakile cutar a jihar, Sanata Baba Tela, ya nuna godiyarsa a bisa kokarin kungiyoyin biyu a bisa wanan tallafi da suka kawo, ya na mai shan alwashin tafiyar da taimakon nasu ta hanyoyin da su ka dace.

Tela ya ce tallafin zai taimaka wajen yaki da cutar da suke kan yi a jihar. Sai ya nemi wasu ma da su yi koyi.

A gefe guda kuma yay aba musu bisa kokarinsu yana mai cewa kungiyar Lauyoyin tana daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawarsu wajen samun nasarar gwamna Bala Muhammad tun daga kan kotun zabuka, daukaka kara har zuwa kotun Allah ya isa, sai ya ce gwamnatin tana sane da irin sa’ayinsu da kokarinsu kan jihar da gwamnati.

 

Exit mobile version