Hukumomin kasar Sin sun bayyana cewa a yau Lahadi an fara sufurin jiragen kasa tsakanin biranen Beijing zuwa Xiong’an, wanda ya hada babban birnin kasar Sin da sabon yankin Xiong’an.
An tsara jirgin kasan zai dinga gudun kilomita 350 a kowace sa’a.
A ranar 1 ga watan Afrilun shekarar 2017, gwamnatin Sin ta tsara shirin kafa sabon yankin musamman na Xiong’an, wanda ya kasance wani muhimmin aiki ne na raya cigaban rukunin biranen Beijing da Tianjin da lardin Hebei domin saukakawa birnin Beijing wajen tafiyar da al’amurransa yadda ya kamata a matsayinsa na babban birnin kasar.
Shugabannin kasar Sin sun yi alkawarin gina sabon yankin Xiong’an bisa amfani da fasahohin zamani, da makamashi mai tsafta, da na’urorin zamani, kuma mafi daraja a duniya. Domin tabbatar da yanayin sararin sama mai launin shudi, da ingantacciyar iska, da ruwa mai tsafta, kana kowane taku guda na duk fadin yankin za a yi masa kyakkyawan tsari mafi dacewa. (Ahmad)