Tare da Baƙir Muhammad
Rob Goldman babban darektan tallace tallace na shafin facebook ne ya ƙaryata wannan zargin, duk da ya amince da batun cewa shafin na sako ma masu tahamulli da shi talla da ta dace da harkokinsu na yau da kullum, amma haka ba komai yake nufi ba, illa kokarin sauƙaƙa wa masu amfani da shafin.
‘Muna sanya tallace tallace a shafinmu na Facebook, amma sam bamu taba amfani da na’urar Magana don satar jin masu amfani da shafin ba, balle mu san mai suka fi buƙata, duk shafukkanmu ciki kuwa harda Instagram ma.’ Inji Goldman.
Mutane da dama sun damu da yadda suke ganin tallace tallace da suke dacewa da harkokinsu na yau da kullum, hakan yasa mutane da dama suke ganin lallai shafin na leƙen sirrikansu don gane tallen da ya dace da su, da harkokinsu na kullum.
Amma facebook sun ƙaryata wannan zargin da cewa suna sako talle ne da ya dace da sha’awar masu tahamulli da shafin, da kuma bayanan da suka sanya a shafin da kansu, daga bayanan muke iya gane tallen da ya dace da kowanne mutum da yake tahamulli da shafinmu.
Duk wasu suna ganin lallai abun ba haka bane sam sam, ana iya sako maka tallace tallace masu yawa amma da yake baka da sha’awar abunda aka sako maka sai ka wuce tallen ma baka damu ba, amma muddin aka ce an sako maka tallen abunda kake sha’awa toh hankalinka zai kai wajen, shafin suna saka tallace tallace masu dama, wasu su ba mutum sha’awa wasu kuwa sam basa ba mutum sha’awa.