Bunkasar Fasahar Sadarwar Zamani A Kamfanin Huawei

Kamfanin samar da fasahar sadarwa ta zamani na Huawei za a iya cewa ya zama gagarabadau a duniya baki daya wajen inganta saukin rayuwa ga Dan Adam.

Sannu a hankali kamfanin yana fadada fasaharsa ta sadarwa zuwa sauran sassan abubuwan more rayuwa masu amfani da makamashin lantarki da makamashin hasken rana.

A ziyarar da LEADERSHIP A Yau ta kai kamfanin a Birnin Shanghai na Kasar Sin, ta ga yadda fasahar Dan Adam ta samu bunkasa fiye da yadda ake tunani saboda sababbin abubuwan da kamfanin ke bullowa da su na cigaban duniya ta hanyar kimiyyar zamani (digitalization).

Kamfanin yana da cibiyoyin bincike da samar da sababbin fasahohin kimiyya guda goma sha hudu a sassan duniya, inda ya ajiye guda takwas a Kasar Sin, baya ga sauran kasashen duniya da ya kafa ofisoshinsa sama da dari da saba’in. Huawei yana da ma’aikata sama da dubu dari da tamanin a duniya. Shi ne kamfani na tamanin da uku a cikin kamfanoni dari biyar da suka yi zarra a fagen cigaba a duniya. Ya kasance na saba’in a cikin kamfanoni dari da suke sarrafa kaya mafi inganci.

Yanzu haka kokarinsa na kara bunkasa fasahar karfin sadarwa daga 4G zuwa 5G ya yi nisa, inda aka kammala aikin kashi na farko. Kamfanin ya kuma kara himmar samar da fasahar da za a rika inganta manhajar sadarwar da ake amfani da ita ba tare da an sauya gangar jikin na’urar da ake amfani da ita ba.

Kayan da Kamfanin Huawei ke samarwa su ne aka fi yin fitonsu a teku a duk fadin duniya inda kamfanin ya kwashe fiye da rabin kashin daukacin kayan sadarwa da ake fitonsu. Fasahar kamfanin na Kasar Sin ba ta tsaya a nan ba, har ila yau ta nausa bangaren samar da lantarki inda yanzu haka ya hada gwiwa da Gwamnatin Ghana wajen samar da fitilun kan hanya masu amfani da makamashin hasken rana mafi inganci, madaidaici (ba mai cika wuri ba) kuma a farashi mai rahusa.

Wakazalika, ba da jimawa ba, kamfanin yana shirin kaddamar da wata sabuwar fasahar kimiyya ta ajiye motoci a wurare daban-daban. Idan aka kamala aikin na’urar sabuwar fasahar, masu motoci za su iya biyan kudin ajiye mota tun daga gida kafin su fito ta hanyar manhajar kwamfuta da kamfanin zai samar. Wadanda za su mori sabuwar fasahar za su kasance babu ruwansu da jiran-tsammani kafin su samu wurin ajiye motarsu, sannan da zarar mutum ya biya kudin ajiye motarsa babu wani mahaluki da zai iya yi ma sa shigar sauri ya ajiye motarsa a inda ya biya.

Wani karin abin sha’awa game da cigaban fasahar zamani da kamfanin ke kirkirowa, ya daura damarar mayar da harkokin wasu birane su zama komai na na’ura. A karkashin haka, duk birnin da aka daukaka darajarsa da fasahar kamfanin, zai zama birnin da za a rika gudanar da rayuwa bai-daya, ma’ana duk abin da mutum yake bukatar yi na’ura kawai zai danna ya samu biyan bukata nan-take-yanke ba sai ya sha wata wahala ba.

Kamar yadda wata jami’ar kamfanin, Ailen Li ta bayyana mana, Biranen Tokyo, Jamus, Shanghai, Honkon da Landan tuni suka rungumi wannan sabuwar fasahar ta mayar da harkokin gudanarwarsu a manhajar fasahar zamani.

Ta fuskar aikin gona, Kamfanin Huawei ya bullo da wata fasaha da take inganta sadarwa a fannin kasuwancin kiwon dabbobi inda ya samar da wata fasaha da masu kiwon shanu ke amfani da ita wurin duba lafiyar dabbobinsu, sanin adadin abincin da ya kamata a rika ba su da sanin lokacin da suka kamu da cuta da ba su magani a sa’ilin da ya dace.

A watan Fabarairun shekarar 2017, Hukumar sadarwar tarho na Kasar Sin ya yi hadin gwiwa da Kamfanin Huawei da na Yinchuan AOTOSOS domin samar da fasahar da za ta inganta sashen kiwon dabbobi na kasar. Wannan ne ya kai ga samar da fasahohin zamani na NB-IoT da UCOWS wadanda suka taimaka gaya wajen bunkasa kula da dabbobin da ake kiwo. Ta hanyar wadannan fasahohin, ana iya tura bayanan da suka shafi ciki da wajen dabbobin da ake kiwo zuwa babbar ma’ajiyar sadarwa ta musamman ta sadarwar Kasar Sin. Ta hakan, masu kula da gidajen gonan da ake kiwon dabbobi, da makiyaya dabbobi da sauran su na iya samun bayanan da suke bukata game da shanu ta hanyar amfani da manhajar waya ko shafin intanet.

Ko wace saniya da ake kiwo akan makala ma ta wata na’urar sadarwa da ta ke ba da rahoton halin da saniya ke ciki sau takwas a kullu yaumin. A sakamakon sabuwar wannan fasahar, kiwon shanu a kasar na samun bunkasa a kimiyance tare da habaka ribar da ake samu da inganta lafiyarsu da madarar da suke samarwa. Har ila yau, fasahar ba ta tsaya a kan amfanar da shanu kadai ba, sauran dabbobi irin su tumaki, dawaki, birai da sauran su za a iya mu su amfania da ita.

Ba wadannan ne kadai ba, Kamfanin Huawei ya inganta ayyukan kafanoni da dama a kan harkokinsu ta fuskar sadarwa irin su DHL, Kamfanin Gas na Sin, Kamfanin samar da ruwa na Australia, tsaron manhajar komfuta ga kamfanoni da dama.

Sauran sassan da kamfanin yake kara taka muhimmiyar rawa a bangaren zamanantar da duniya sun hada da sanya wa motoci giyar latsawa ta gefen sitiyari mai karfin 5G, bude fagen tallata kasuwanci a zamanance, bunkasa aikin mutum-mutumi a kamfanonin kere-kere da sauran fasahohin sadarwa na zamani bila’adadin.

Kamfanin Huawei ya lashe lambar yabon zama gwarzon kamfanin sadarwa na duniya da aka bayar a wannan shekarar ta 2018.

 

Exit mobile version