LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya

byYusuf Shuaibu
7 months ago
Hausa

A ranar Talata, 25 ga Fabrairu, 2025, Jaridar LEADERSHIP ta gudanar da bikin karrama wadanda suka lashe gasar rubuta gajerun labaran soyayya ta Hausa ta hanyar kiran bidiyo na WhatsApp. Wannan gasa an shirya ta ne domin karfafa gwiwar ga masu bibiyar LEADERSHIP HAUSA tare da bunkasa fasahar rubutu a cikin al’ummar masu magana da harshen Hausa.

Taron ya samu halartar jagororin LEADERSHIP, ciki har da Shugaban Sashen Dijital, Mista Samuel Ossai, Editan LEADERSHIP HAUSA, Malam Bello Hamza, Shugaban Sashen LEADERSHIP HAUSA Online, Muhammad Bashir Amin, da kuma Manajan Soshiyal Midiya, Malam Naziru Adam Ibrahim.

  • Hukuma Ta Rufe Gidajen Gala A Jihar Kano
  • Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Janye Bincike Kan Shigo Da Jan Karfe

Gasar ta bayar da kyaututtuka na kudi ga wadanda suka yi nasara: N50,000 ga wanda ya zo na farko, N25,000 ga wanda ya zo na biyu, da N10,000 ga wanda ya zo na uku. Alkalan gasar, karkashin jagorancin Muhammad Bashir Amin, sun tantance labarai bisa la’akari da kirkira, asali, da kuma ingancin labari.

A jawabinsa, Editan LEADERSHIP HAUSA, Malam Bello Hamza, ya taya dukkan mahalartan murna tare da karfafa musu gwiwa kan ci gaba da bibiyar dandalin LEADERSHIP HAUSA. Haka nan, Shugaban Sashen Dijital, Mista Samuel Ossai, ya yaba wa alkalan gasar da wadanda suka yi nasara.

Zainab Muhammad, wacce ta zo ta biyu, ta yi jawabi a madadin masu nasarar, inda ta nuna godiyarta ga LEADERSHIP HAUSA bisa wannan dama da suka samu, tare da alkawarin ci gaba da tallafa wa jaridar a shirye-shiryenta.

Wadanda Suka Yi Nasara

Aliyu Usman Adam – Matsayi na daya

Aliyu Usman Adam, dan asalin Zariya ta Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a 2008. Bayan hidimar kasa a Jihar Edo, ya yi aiki a kamfanin SAN Yoghurt da kuma Alhuda Center School daga 2011 zuwa 2014.

A 2014, Aliyu ya koma aikin jarida, inda ya yi aiki da jaridar RARIYA a Abuja har zuwa 2017. A halin yanzu, shi ne Manajan shirye-shirye (Content Manager) a Nishadi TB Abuja. Yana da mata da ‘ya’ya biyu.

Zainab Muhammad (Indian Girl) – Matsayi Na Biyu

Zainab Muhammad, wacce aka fi sani da “Indian Girl,” ‘yar asalin karamar hukumar Dala ce a Kano. Ta kammala firamare da sakandare a Kano, tare da burin ci gaba da karatun jami’a a nan gaba.

Zainab tana da kwazo a bangaren ilimin addinin Musulunci, kuma tana amfani da kafafen sada zumunta wajen ilmantarwa da fadakarwa. A halin yanzu tana da tarin masoya saboda rubuce-rubucenta masu kayatarwa da gina al’umma.

Mujaheed Nuhu Yusuf (Mujaheed Matashi) – Matsayi Na Uku

Mujaheed Nuhu Yusuf, wanda aka fi sani da Mujaheed Matashin marubuci ne a fagen wasan kwaikwayo kuma mawaki daga Kano. Ya wallafa littattafai biyu na wakoki, ciki har da Philosophy Mysterious Pen, wanda ya wallafa tare da marubuci Haiman Ra’ees.

Mujaheed shi ne shugaban kungiyar marubuta Ruhin Adabi, kuma yana wallafa rubuce-rubucensa a shirin Bakandamiya Hikaya da kuma shafinsa na Facebook.

Wannan gasa ta kara tabbatar da aniyar LEADERSHIP HAUSA na bunkasa hadaka da kirkirar rubutu a cikin al’ummar Hausawa. Jaridar na shirin ci gaba da shirya irin wadannan gasar domin karfafa sha’awar adabi da kuma karfafa dangantaka da masu karatu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja
Labarai

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
Next Post
Maraba Da Watan Ramadan

Maraba Da Watan Ramadan

LABARAI MASU NASABA

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version