LEADERSHIP Na Taka Rawar Gani Ga Jami’an Tsaro —Kwamishinan ‘Yan Sanda

Daga Wakilinmu

Sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Sadiƙ Abubakar Bello ya yaba wa kamfanin rukunan jaridun LEADERSHIP bisa irin gudummawar da jaridun kamfanin ke bayar wa ga jami’an tsaro a aikinsu na tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya a ƙasa.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wata ziyarar sada zumunci da ya kai hedikwatar kamfanin LEADERSHIP da ke Abuja, a shekaran jiya Juma’a. inda ya  ƙara da cewa ya kawo wannan ziyarar ne domin neman ƙarin haɗin kan jaridar LEADERSHIP domin ci gaba da tabbatar da tsaro, sannan kuma tare da yiwa jami’an ‘yan sandan gyara a wuraren da aka ga sun yi ba daidai ba.

Bello ya ce: “Mun yaba da irin gudummawar da kamfanin LEADERSHIP ke ba jami’an ‘yan sanda. Tare da samun haɗin kanku ne za mu iya gudanar da ayyukanmu na tabbatar da tsaro. Kuma wannan ziyara mun kawo ta ne don muna son yin aiki kafaɗa da kafaɗa da dukkan ɓangarorin al’umma.

“A shirye muke mu yi haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a dukkan ɓangarorin ayyukanmu. Saboda haka, ƙofofinmu a buɗe suke don amsan shawarwari, ƙorafe-ƙorafe da bahasin yadda muke gudanar da ayyukanmu, domin mu gyara.” Inji kwamishinan.

A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa, mai masaukin baƙi, kuma Babban Manajin Daraktan Rukunan Kamfanin LEADERSHIP, Abdul gombe ya fara ne da yi wa tawagar kwamishinan barka da zuwa kamfanin jaridar. Tare kuma da taya shi murnar sabon muƙamin da ya samu na kwamishinan ‘yan sanda a Babban Birnin Tarayya. Haka kuma Abdul Gombe ya shaidawa Kwamishinan cewa kamfanin LEADERSHIP a shirye yake ya ci gaba da ba jami’an ‘yan sanda gudummawa kan ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Babban Manajin Daraktan ya ce: “Rukanan Kamfanin LEADERSHIP na wallafa jaridun turanci waɗanda suka haɗa da LEADERSHIP ta kullum, LEADERSHIP ta Juma’a, LEADERSHIP ta Asabar, da kuma LEADERSHIP ta Lahadi. Sannan kuma a ɗaya ɓangaren muna buga jaridar MDA’s wanda ke fitowa duk wata.

“Makonnin baya muka ƙaddamar da jerin jaridun hausa, wanda ke fitowa kullum, irinta ta farko a tarihin Nijeriya. Jaridun sun haɗa da: LEADERSHIP A Yau, wacce ke fitowa kullum (daga Litinin zuwa Alhamis), da LEADERSHIP A Yau Juma’a, da LEADERSHIP A Yau Asabar, da LEADERSHIP A Yau Lahadi.” Inji shi

Daga ƙarshe Babban Manajin Daraktan, ya jaddadawa Kwamishinan cewa cikin abubuwan da waɗannan jaridun kamfanin LEADERSHIP za su muhimmanta akwai wayar da kan al’umma dangane da muhimmancin tsaro da kiyaye doka.

Exit mobile version