LEADERSHIP Ta Karrama Shugaban JAMB A Matsayin Gwarzon Shekara

A halin yanzu da misalin karfe 12:42pm wanda LEADERSHIP ke karramawa a dakin taro na ICC dake Abuja, shi ne Farfesa Ishaq Olanrewaju Oloyede, a matsayin gwarzon shekara.

Inda Kamfanin suka karrama shi da kyauta. Inda ya fito ya karbi kambunsa.

Ya samu wannan karramawar ne duba da yadda yake ba da gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya a ma’aikatarsa.

Bayan karrama shi, ya nuna jindadinsa, sannan aka yi jawabin godiya da kuma kada taken Nijeriya.

A halin yanzu ana daukar hotuna ne kafin a watse. Taron a halin yanzu an karkare dukkanin muhimman abin da ya tara jama’a da misalin karfe 12: 49.

Exit mobile version