LEADERSHIP A YAU: Gabatar Da Jaridar Hausa Ta Farko Mai Fitowa Kullum A Nijeriya

A gobe Litini ne(11/9/2017) kamfanin buga jaridun LEADERSHIP, karkashin shugabancin zakakurin marubuci, dan kishin kasa, Sam Nda-Isaiah, wanda kuma ba karamar gudumawa yake bayarwa ba wajen ci gaban kasar nan, musamman a harkar aikin jarida ya shirya tsafa domin kafa tarihi a fannin jaridar Hausa a duniya.

Inda zai fara buga jaridar Hausa mai fitowa kullum, wacce aka rangada mata suna LEADERSHIP A YAU, za ta zama makwafin LEADERSHIP HAUSA ce, wacce aka kwashe ’yan makwanni ba ta fito ba saboda shirye-shiryen fitowar wannan sabuwar jaridar mai sabon tsari.

Domin tafiya da tare da zamani, jaridar ta zo da sabon salo, inda za ta kunshi mai fitowa kullum, daga Litinin zuwa Alhamis (LEADERSHIP A Yau). Sannan akwai LEADERSHIP A Yau (Juma’a), wacce ita kuma za ta rinka fitowa ne duk ranakun ne Juma’a. Haka nan kuma akwai wacce za ta rinka fitowa a duk ranar Asabar (LEADERSHIP A Yau, Asabar) da kuma wacce za ta rinka fitowa a ranar Lahadi (LEADERSHIP A Yau, Lahadi).

Muna farin cikin sanar da dimbin masu karatunmu cewa wannan sabuwar jarida tana dauke da muhimman abubuwa masu ilimantarwa, Fadakarwa, nishadantarwa da al’amura na zamantakewar yau da kullum. Duk wadannan suna nan tafe cikin sabon salo da tsari ingantacce.

Za a iya ziyartarmu a adireshinmu na yanar gizo www.leadershipayau.com

LEADERSHIP A Yau, Don Allah Da Kishin Kasa.

 

 

Exit mobile version