Daga Hussani Baba
Shugabar Kwalejin kimiya da fasaha ta horar da malamai ta gwamnatin tarayya da ke Gusau Wato (FCET) Dakta Baraka Abukabar, ta bayyana cewa, “Kafanin Jaridar Leadership ya kafa tarihi a Kasar nan na samar da jaridar Hausa mai fita kowacce rana, Wato Leadership A yau. Wannan babban kokari ne da Kamafanin ya yi, kuma ya zama zakaran gwajin dafi, dole a yaba masa, kuma wannan jarida za ta taimaka wa daliban Kwalejin horas da Malamai musamman tsangayar Hausa”.
Kamar yadda tsangayar ke takama da jaridun Ingilishi wajen kara kwarewa na iya harshe. Wannan jaridar Leadership A Yau ita daliban tsangayar Hausa da ma wadanda ke san iya karatun Hausar zai taimaka musu wajen kwarewa da fahimtar harshen. Dakta Baraka ta bayyana haka ne a lokacin da take zanta wa da wakilinmu a ofishinta da ke Kwalejin a Gusau.
Dakta Baraka ta kara bayyana cewa, “Jaridar Leadership A Yau da ga yau ta samu shiga dakin karatun Kwalejin, mun sa ta a cikin sahun jaridun da muke saye kuwace rana, kuma suma tsangayar Hausa mun ba su umarnin sayenta kodayaushe don amfanar dalinbai”. Shugabar ta yi wa jaridar tsokaci a kan Kwalejin kimiyya da fasaha ta mata zalla da take wa shugabanci kamar haka “Kwalejin Kimiyya da fasaha ta mata ta gwamnatin tarayya da ke Gusau jihar Zamfara a fadin Afirka ta yamma wannan Kwalejin ita kadai ce ta mata zallah. An yi ta ne don horas da malami kimiyya da kere-kere, ganin cewa, akwai karancin dalibar wadannan tsangaya ne ya sa Kwalejin ta kara tsangayoyin koyan harsuna da aikin gona, da kasuwanci da lissafi da dai sauran su, kuma yanzu haka Kwalejin na da isassun kayan aiki da Kwararun malamai da dalibai Sama da dubu biyar. Babban kalubalen da take fuskanta shi ne rashin dalibai, akwai bukatar a samu dalibai dubu goma sha biyar, ban da karatun NCE, an fara Digiri Wanda a kai hadin gwiwa da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya yau shekara uku kenan da fara Digiri a Kwalejin.
Sannan Kwalejin na iyaka kokarinta na ganin jindadin dalbai da malamai da tura malaman karo karatu da kuma zuwa kwasa-kwasai.
A Karshe, Dakta Baraka ta yi kira ga jahohin da ke makwabtaka da Kwalejin irin su Katsina da Sakkwato da Kebbi da su daure su turo ‘ya’yans u mata zuwa wannan Kwaleji domin kwalejin ta mata ce zalla, don ku amfana da kasancewar makarantar a wannan yanki.