Jaridar “Leadership” ta Najeriya ta wallafa wani bayani da Issa Aremu ya rubuta, mai taken “Kara kyautata huldar dake tsakanin Najeriya da Sin cikin shekaru 50 masu zuwa.” Cikin bayanin, Issa Aremu, ya kwatanta hanyoyin da kasashen Najeriya da Sin suka bi don neman raya kansu. A ganinsa, dalilin da ya sa ake samun bambanci sosai tsakanin kasashen 2 ta fuskar ci gaban tattalin arziki shi ne, zabin mabambantan hanyoyin raya kasa da kasashen suka yi.
Malam Issa ya kara da cewa, kasar Sin wata babbar kasa ce mai tasiri a duniya. Kuma duk wanda yake yunkurin neman ta da zaune-tsaye a kasar, sam ba zai samu nasara ba. Ya ce zuwa yanzu, kasar Sin dake bin tsarin siyasa na gurguzu ta riga ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kana ta samu shawo kan yaduwar cutar COVID-19 cikin nasara. Ya kara da cewa, Najeriya da Sin duk kasashe ne masu tasowa, amma hakika akwai gibi sosai tsakanin kasashen, a fannin neman ci gaba. A cewarsa, kasar Sin ta zabi turba mai dacewa a kokarinta na raya kanta, tare da nuna wa mutanen duniya irin nasarorin da kasa za ta iya samu, muddin tana da hakuri da jajircewa, da kokarin sauke nauyin dake wuyanta.
Har ila yau, Malam Issa ya kara da cewa, zuwa bana, kasashen Najeriya da Sin sun kwashe shekaru 50 suna kokarin kyautata huldar diplomasiya a tsakaninsu, lamarin da ya shaida cewa kasar Sin aminiyar Najeriya ce, wadda za a iya dogaro da ita. Ya ce ya kamata Najeriya a nata bangaren, ta zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da Sin, da koyon fasahohin kasar a fannin raya kasa. (Bello Wang)
Muradun Raya Kasar Sin Sun Baiwa Duniya Tabbacin Bunkasuwa
Daga CRI Hausa A yau Juma’a ne aka bude taron...