Abba Ibrahim Wada" />

Leceister City Ta Gayawa Arsenal Farashin Dan Wasa Maddison

Kungiyar kwallon kafa ta Leceister City ta bayyanawa Arsenal cewa idan har tanason siyan dan wasanta na gaba sai ta biya fam miliyan 60 wanda hakan ake ganin dole Arsenal zata hakura da neman dan wasan.

Burin Arsenal na samun tikitin zuwa gasar cin kofin zakarun turai na shekara mai zuwa ya gamu da cikas ne bayan da sukayi rashin nasara a wasan karshe na kofin Europa a hannun Chelsea inda suka dokesu daci 4-1 a ranar Laraba.

Wannan dalili na rashin buga kofin zakarun turai zai tilastawa Arsenal canja lissafin siyan ‘yan wasa kuma tuni aka bayyana cewa idan har bazasu buga kofin zakarun turai ba shugabannin kungiyar bazasu bayar da kudi masu yawa ba domin siyan manyan ‘yan wasa.

Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana Arsenal ta nuna aniyarta ta siyan dan wasa Maddison wanda tauraruwarsa ta haska a kungiyar Leceister City a kakar wasan data gabata duk da cewa ba Arsenal bace kawai take zawarcin dan wasan.

Leceister dai ta bayyana cewa bazata saurari kowacce kungiya ba idan har bazata taya dan wasan nata ba fam miliyan 60 wanda hakan zaisa Arsenal ta hakura da neman dan wasan domin yayi mata tsada idan akayi la’akari da kudin da aka warewa kungiyar na siyan sababbin ‘yan wasa.

Shugabannin kungiyar Arsenal dai sun ware fam miliyan 45 ga mai koyarwa Unai Emery dominya siyi ‘yan wasa dasu sakamakon basu je kofin zakarun turai ba sai dai sun bashi dama ya siyar da wasu daga cikin manyan ‘yan wasan kungiyar kamar irinsu Ozil.

Bayan an tashi daga wasan da sukayi rashin nasara a hannun Chelsea ne dai kociyan na Arsenal, Emery, ya bayyana cewa idan har kungiyar tanason ta cigaba da fafatawa a gasar firimiya dole sai sun siyi manyan ‘yan wasa matakin da ake ganin abune mai wahala kuniyar ta iyayi a yanzu duba da tun farko kudin da suka ware.

Exit mobile version