Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City ta sallami kocinta Craig Shakespeare ɗ an ƙasar ingila watanni hudu bayan da ya saka hannu kan yarjejeniyar jan ragamar kungiyar shekara uku.
Shakespeare mai shekara 53, ya maye gurbin Claudio Ranieri, ɗ an ƙasar Italiya a watan Fabrairu, wanda kungiyar ta kora bayan da ya kasa taka rawar gani duk da cewa ya lashe kofin firimiya.
Bayan da Shakespeare ya tsallakar da Leicester daga hadarin barin gasar Premier a bara ne inda kungiyar ta yi ta 12 a kan teburin gasar ya sa aka ba shi aiki a watan Yuni wanda hakan yake nufin mahunkantan ƙungiyar sun amince da kamun ludayinsa.
Leicester City tana ta 18 a kan teburin Premier bana, kuma ba ta ci wasa ba a karawa shida da ta yi a jere, bayan da aka buga fafatawar mako takwas a gasar.