Sabo Ahmad" />

Leda Ta Zama Alakakai Ga Al’ummar Kasar Nan

Rana irin ta jiya biyar ga watan Yuni aka ware musamman domin yin bikin ranar muhalli a sassa daban-daban na duniya. Sharar leda dai ta zama alakakai ga al’ummar kasar nan musamman ma Arewacin kasar nan.

Bayan da majiyarmu ta samo mana, sun tattaki zuwa lunguna da sakuna musamman na jihar Kaduna domin jin yadda lwda ta yi tasiri a cikin al’umma da kuma ililonta.

A unguwar Tudun Wada Kaduna, an gano a kowace rana akwai shagon da kan bayar da akalla  leda guda dari daya ga kwastomominsa don su sanya kayan da suka saya. Mai shagon ya taba yunkurin takaita ya bayar da leda amma kuma sai hakan ya korar masa kwastoma: “Wani kostomana rigimi muka yi da shi kan batun na leda.”

To sai dai ga Habiba Ibrahim mai sayar  da ganyen ogu da sauran kayan miya a kasuwar Barci Kaduna, ita ba ta taba yin sa-in-sa da kwastoma akan leda ba. Amma kuma tana kashe kudi sosai wurin biya wa masu siyan kayanta bukatarsu: “Ina kashe kudade da yawa kafin na sayar da kayan saboda sa wa a cikin leda.”

Da alama dai akulli yaumin bukatar leda karuwa take. Adamu Mudi, wani magidanci, ya shaida wa wakilinmu cewa ba zai iya yin sayayya ba tare da an sanya masa leda ba saboda sirrinta abin da ya saya.

“Kamar wannan leda idan na gama aiki da ita ina sata a kwandon shara, wata kuma na sake amfani da ita, akwai dai sirri.”

Irin yadda ake jefar da ledoji a wurare daban-daban masana irinsu Dakta Yusuf Sale na jami‘ar jihar Kaduna na cewa akwai illa matuka domin leda na dauke da wasu sinadarai masu lahani ga dan’adam:

“Leda kan haifar da matsala ga muhalli idan ma ta ragargaje a kasa ta kan shiga kasa ta haifar da illa ga dan’adam.“

A  cewar masana sinadaran da ke tattare da leda a wasu lokuta har cutar daji ma suke sababawa. To sai dai da alama wannan ba zai sauya ra’ayin Hamisu kudan ba wanda ya ce ya sani da haka amma yana matukar bukatar ta ledar a harkokinsa.

A watan da ya gabata ‘yan majalisar dokokin Nijeriya sun zartar da kudurin da zai takaita amfani da ledar, kuma masu fafutukar kare muhalli na son ganin gwamnatin Nijeriya a wannan sabon zangon nata ta magance matsalolin da leda ke haifarwa ga mutane.

Exit mobile version