Legas: An Cafke Dan Sandan Bogi Da Wiwi

Magidanci

Bongani Moyo seconds after hearing that he will probably never leave jail again. Picture: Oupa Mokoena

Daga Rabiu Ali Indabawa,

Rahotanni daga Jihar Legas, sun zo da ingaci kan ‘Yan sanda a jihar sun yi nasarar damke wani dan sandan bogi, Dabid Omoruyi da tabar wiwi.

Wanda aka cafke din, Omoruyi, an kama shi tare da katin shaidar dan sanda na bogi, inda kuma ya tabbatar da cewa shi ba dan sanda bane. Kwamishinan yan sandan Legas ya ba da umurnin a mika shi ga sashen masu binciken manyan laifuka wato CID ‘Yan sandan Area E Command a Festac Jihar Legas ne suka kama wannan matashi Dabid Omoruyi, mai shekara 37 mazaunin No 4 Job Street Afromedia, Oto-Awori LCDA saboda laifin yi wa ‘yan sanda sojan gona, kamar yadda jaridar Banguard ta ruwaito.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Olamuyiwa Adejobi, ya ce an kama Omoruyi dauke da katin shaidar dan sanda na bogi da kuma wani ganye da ake zargin tabar wiwi ce mai nauyin kilogram 30.

“An gano Omoruyi dauke da wasu jakunkunan tabar Wiwi a kasuwar ne Alaba, Ojo da ke Legas yana gudu tare da abokansa kafin a kama shi. “Omuruyi ya yi ikirarin cewa shi dan sanda ne mai mukamin saja da ke aiki tare da Mopol 49, a Jihar Legas, amma a yayin da ake masa tambayoyi a caji ofis ya amsa cewa shi dan sandan bogi ne,” in ji Adejobi.

Ya amsa cewa yana amfani da takardar shaidar ta bogi domin safarar miyagun kwayoyi zuwa duk inda ya ke so a jihar. Adejobi ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hakeem Odumosu ya umurci DPO na yankuna su kara mayar da hankali don inganta tsaro a jihar.

“Odumosu ya umurci a mika wanda ake zargin zuwa sashen masu binciken manyan laifuka da ke Panti Yaba domin zurfafa bincike. “Odumosu ya kuma umurci jami’an ‘yan sanda su kamo sauran wadanda suka gudu domin su fuskanci hukunci. “Har wa yau, Odumosu ya gargadi al’umma su rika taimakawa ‘yan sanda da bayyanai masu amfani domin su rika gudanar da ayyukansu yadda ya kamata,” inji Adejobi.

Exit mobile version