Legas: An Gurfanar Da ’Yar Kasuwa A Kotu Bisa Satar Jariri

An gurfanar da wata ‘yar kasuwa mai suna Immaculate Otam ‘yar shekara 35 da haihuwa, a gaban kotun Jihar Legas wacce ta ke da zama a garin Ikeja, bisa zargin ta da satar jariri dan wata guda. Ita dai Otam, ta na zaune ne a yankin Okota cikin Jihar Legas, ta na dai fuskantar tuhuma guda biyu na tada zaune-tsaye da kuma laifin sata, wanda ta musanda laifin da a ke tuhumar ta da shi.

Da ya ke yi wa kotu bayani, lauya mai gabatar da kara Edet Akadu, ya bayyana cewa, Otam ta aikata wannan laifin ne a ranar 29 ga watan Yuli, a gida mai lamba 299 da ke kan titin Agege Motor cikin yankin Mushin ta Jihar Legas. Ya zargi wacce a ke tuhuma da tada zaune-tsaye, inda ta shiga gidan Mista Badmus, sannan ta sace jariri sabon haihuwa, sai dai an samu nasarar damke ta. Akadu ya kara da cewa, wannan laifi ne da ya saba wa sashe na 278 da 168 na dokokin manyan laifuka ta Jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa, sashe ya tanadi hukuncin daurin watanni uku a gidan yari ga duk wanda a ke kama da laifin sata.

Alkali mai shari’a, Mista K. O. Ogundare, ya bayar da belin wacce a ke tuhuma a kan kudi na naira 200,000 tare da mutum biyu masu tsaya mata. Ya kuma dage sauraron wannan kara har sai ranar tara ga watan Oktoba.

Exit mobile version