Yusuf Shuaibu" />

Legas: Mutane Sun Lakada Wa Mai Satar Mutane Kashin Tsiya

A makon da ta gabata ce, mutane su ka nakada wa wani matashi wanda a ke zargin sa da yin garkuwa da mutane kashin tsiya, a yankin Iyana Ipaja cikin Jihar Legas. A na dai zargin sa da yin garkuwa da wani yaro wanda ya ijiye a cikin buhu.

Wani wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa ya bayyana cewa, nan take a ka damke shi bayan mutane sun fahimci abinda ya ke cikin buhun, inda a ka ciro yaran tare da tube masa riga, sannan mutane su ka yi masa mummunar duka. Ya kara da cewa, “mun lura ya na rige da buhu wanda ya ke dauke da karamin yaro. Mun tambaye shi a kan manufarsa, ya ki ba mu amsa. “Nan take a ka sanar wa da mutane da ke wurin. Mutane sun taru sosai a wannan wurin, inda a ka fara dukan sa har sai da a ka yi masa mummunan rauni.”

An bayyana cewa, wanda a ke zargin mai garkuwa da mutane ne ya zo garin Ibadan babbar birnin Jihar oyo.

Majiyarmu ta ruwaito mana cewa, daga baya an mika wanda a ke zargin ga ‘yan sanda, yayin da a ka mika yaron da a ka yi garkuwa da shi ga mahaifiyarsa.

Exit mobile version