Umar A Hunkuyi" />

Legas Ta Tara Naira Bilyan 25 Duk Da Dokar Kullen Korona

Hukumar tara kudaden haraji ta Jihar Legos ta tara Naira Bilyan 25 ta hanyar tara kudaden haraji a watan Afrilu, duk da dokar kulle da ke aiki a wancan lokacin, shugaban sashen sadarwa da yada labarai ta yanar gizo na hukumar, Mista Rasheed Olu-Ajayi, ne ya fadi hakan a ranar Asabar.

Olu-Ajayi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa hukumar ta kai ga nasarar hakan ne ta hanyar yin amfani da kimiyyar zamani.

Ya ce, duk da cewa abin da suka taran bai kai ga abin da suka tsammaci iya Tarawa ba, amma dai hakan ya fi a ce ba su iya tara komai ba in aka yi la’akari da yanda aka kulle komai a wancan lokacin.

“Abin da muka yi shi ne, mun ci gaba da gudanar da ayyuka ne ta hanyar taskace duk wasu bayanai na kayayyaki da sauarnsu wanda muka ci gaba da yin aiki a kansu,” in ji shi.

“Sai muka yi amfani da hanyoyin kimiyyar zamani, inda kuma ma’aikatanmu masu yawa duk su ke ci gaba da gudanar da ayyukansu daga gidajensu wajen neman masu biyan harajin.

“Mun iya tara kudade masu yawa, ba wai mu koma Tarawa ne ba a halin yanzun daga babu komai a kasa.

Exit mobile version