Gwamnatin jihar Legas ta ce za ta kafa makarantar horar da mahauta a jihar, inda ta yi nuni da cewa, idan aka aiwatar da Makarantar za ta kasance ta farko da aka taba kafawa a jihar.
Gwamnatin ta ce shirin shi ne a horar da mahautan, sababbi da kuma dalibai na yanzu kyawawan dabaru yanka dabbobi na duniya tare da harkar yanka.
Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jiharAbisola Olusanya ce ta sanar da hakan a yayin gwajin wani sabuwar mahautan da aka yanka na shanu da akuya a karkashin daka da jama’a da masu zaman kansu a yankin Bariga na jihar.
Kasuwancin mahauta ya kunshi tsarin yanka dabbobi da shiryasu don sayarwa ga masu amfani a nama.
A cewar Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya, muna so mu fara kawo wadanda suka kammala karatu da kuma matasa don su kasance ana tsarawa da yankawa kuma hanya daya ce tilo da za ta ja hankalin matasa a wannan fannin ita ce ta samar da mahautan da ke da injina da kuma injina.
Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya ta kara da cewa, ba za mu iya kawo su cikin yanka irin na gargajiya dake kan tsafta ba, mai kyau kuma ba ya jan hankalin abokan huldar mu da za su biya kudn kuma hakan zai sanya wannan bangare ya zama mai jan hankali ga mutane.
Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya ta yi nuni da cewa, makarantar, idan aka aiwatar da ita kamar yadda gwamnatin Legas ta ce, za ta kasance irinta ta farko a kasar.
A cewarKwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya, kasuwancin yana zama mai riba yayin da samar da karin dama ga darajar sashin, inda ta ci gaba da cewa, saboda a haka, kafa makarantar kimiyya da alama ya zama dole yayin da gwamnatin jihar ke neman fadada da kuma daidaita bangaren.
A bisa kokarin sa na daidaita kasuwancin yankan dabbobi a jihar, Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya ta ce, a kwanan nan gwamnati ta kafa wata tawaga da ta fatattaka wuraren yanka dabbobi ba bisa ka’ida ba, kula da kuma aiwatar da manufofin da suka shafi safara da sayar da jan nama a jihar.
Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya ta kara da cewa, mahimmancin horar da mahautan da kuma rungumar fasahar zamani a bangaren.
A cewar Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya, nauyi ne a kanmu a matsayinmu na gwamnati don tabbatar da cewa mun horar da mahautan da muke da su sannan kuma mu nuna wa sabbin mahautan cewa wannan shi ne tsarin.
Da ta ke tsokaci kan inganci da karfin sabuwar mahautan ta ce, mahautan za su iya aiki a karshen shekara, inda ta bayyana cewa, “Layin na kusa da inji yana ba da wani yanki na tsaka-tsaki da sassauci tsakanin abin da ya riga ya kasance da abin da muke son zuwa, inda ta ce, saboda haka abin da za mu ci gaba zai kasance ne mai hade da injunan da ba su da injinan gudanar aiki.
A cewar Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya da ma wannan mahautan yakamata su samar da ayyukan yi kai tsaye sama da mutane 500 da kuma samar da aikin kai tsaye na wasu karin mutane 1,000.
Kwamishiniyar Ma’aikatar Aikin Noma ta jihar Abisola Olusanya ta bayyana cewa, don haka a wannan wurin kadai, ya kamata ya kasance ana da ayyukan samar da aiki tsakanin mutane 1,500 zuwa 2,000.