Lewandowski Na Shirin Karya Tarihin Ronaldo

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Robert Lewandowski yana fatan kafin a kammala kakar wasa ta bana ya karya tarihin shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai na bana.

Wannan dai wata kaka ce da Robert Lewandowski ke haskakawa cikinta, ya zuwa yanzu kuma ya ci kwallaye da dama sai dai dan wasan ya dage kan cewa shi ba burinsa ya kamo tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa ba, bayan nasarar da kungiyarsa Bayern Munich ta samu na tsallakawa zagayen daf da kusa da na karshe a gasar zakarun Turai.

Dan wasan kasar Poland din mai shekara 31 a duniya ya zura kwallo biyu a lokacin da Munich ta yi raga-raga da Chelsea a ranar Asabar da ci 4-1 wanda jumullar kwallayen sun zama 7-1 kenan idan aka hada da wasan da aka buga a gidan Chelsea.

Lewandowski ya ci kwallo 13 a wasa bakwai da ya buga na gasar zakarun turai ta Champions League a wannan kakar, kuma kwallaye hudu ne tsakaninsa da tarihin da Ronaldo ya kafa na cin kwallo 17 a kaka daya a gasar, a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014 lokacin yana Real Madrid.

Idan Bayern Munich ta je wasan karshe da za a buga a birnin Lisbon, dan wasan zai buga wasanni biyar kenan har na karshe wanda karin dama ce wajen haye tarihin Ronaldo wanda a yanzu yake Juventus.

“Ba iya kokari na ba ne muna da sauran wasannin da za mu buga a wannan zagayen na siri daya kwale, kawai ina farin ciki kan yadda muke samun dama kuma muna cin kwallo.” In ji dan wasan lokacin da aka tambaye shi game da tarihin Ronaldo.

Lewandowski zai iya kusantar tarihin koma ya haura shi, to amma yana da sauran aiki a gabansa na kamo dan wasan gaban Juventus din kafin ma ya haura shi duk da cewa yanayin yadda yake buga wasa a halin yanzu ba babban aiki bane a gabansa.

Dan wasan Portugal din shi ne ya fi ko wane dan wasa cin kwallo a gasar zakarun Turai, in da yake da kwallo 130  kwallo 64 kenan tsakanin shi da Lewandowski, wanda ya koma na hudu cikin jerin wadanda suka fi cin kwallo a gasar bayan kwallayen da ya ci Chelsea.

 

Exit mobile version