Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da tawagar kwallon kafar kasar Poland, Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa mafi shahara a duniya na Fifa a shekarar nan ta 2020 mai karewa.
Dan wasan ya yi takara ne tare da dan kwallon tawagar Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo da kuma Lionel Messi na Barcelona da tawagar Argentina wadanda a baya sune suka mamaye gasar suke dauka a tsakaninsu.
Dan kasar Poland din, ya ci kwallaye 35 a wasanni 47 a bara da hakan ya taimaka wa Bayern Munich ta lashe kofi uku a kakar da ta wuce kuma Lewandowski, mai shekara 32, shi ne ya zama kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga da kofin kalubale na Jamus da na Champions League a bara.
Wannan ne karon farko da Lewandowski ya lashe kyautar da ya takara da dan kwallon Barcelona. Messi da na Juventus, Cristiano Ronaldo wadanda za’a iya cewa sun lashe kyautar a baya da yawa.
Sannan ‘yar wasan mata Lucy Bronze ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar wasan kwallo ta mata, ‘yar kwallon Manchester City da tawagar Ingila, Lucy Bronze ta lashe kyautar macen da ba kamarta a kwallon kafa a shekarar 2020.
Wadanda suka yi takara:
Lucy Bronze (Manchester City da Ingila)
Pernille Harder (Chelsea da Denmark)
Wendie Renard (Lyon da France)
Shima Jurgen Klopp shi ne kocin kungiyar kwallon kafa ta maza da ya yi fice kuma ya lashe kyautar karo na biyu a jere kenan bayan da a shekarar bara ya lashe bayan ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun turai.
Wadanda suka yi takara:
Marcelo Bielsa (Leeds)
Hans-Dieter Flick (Bayern Munich)
Itama Sarina Wiegman ita ce macen da ba kamarta a horar da kwallon kafar mata kuma mai koyarwa Sarina tana horar da tawagar kwallon kafar Netherlands ne tawagar da tayi abin azo a gani a shekarar data gabata.
Wadanda suka yi takara:
Emma Hayes (Chelsea)
Jean-Luc Basseur (Lyon)
Sarina Wiegman (Netherlands)
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Son Huen-min shi ne ya lashe kyautar kwallon da aka ci mafi kayatarwa kumaSon Heung-min ne ya lashe kyautar Puskas, sakamakon kwallon da ya ci kungiyar Burnley a kakar data gabata.
Wadanda suka yi takara:
Son Heung-min (Tottenham b Burnley)
Luis Suarez (Barcelona da Mallorca)
Manuel Neuer (Bayern Munich da Jamus)
Jan Oblak (Atletico Madrid da Slobenia)
Sarah Bouhaddi ta zama mace mai tsaron raga da tayi fice a shekarar 2020 kuma mai tsaron ragar ta kungiyar kwallon kafa ta Lyon da tawagar Faransa, Sarah Bouhaddi ta zama mace mai tsaron raga da ta yi fice a 2020.
Wadanda suka yi takara: