Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Lewandowski Ya Cancanta Ya Zama Gwarzon Fifa – Flick

by Muhammad
December 1, 2020
in WASANNI
3 min read
Lewandowski
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Abba Ibrahim Wada

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Hansi Flick, ya bayyana cewa ban wasan kungiyar, Robert Lewandowski, shi ne ya cancanta ya lashe kyautar gwarzon ban wasan hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

samndaads

A satin daya gabata hukumar kwallon kafa ta Fifa ta fitar da sunayen ‘yan wasan da za a tantance gwarzon ban wasan bana inda mai tsaron bayan Liverpool, Virgil van Dijk da Mohammed Salah da Sadio Mane da kuma Thiago Alcantara na cikin jerin sunayen ‘yan wasan Liverpool da ke takarar lashe kyautar.

Shi ma ban wasan tsakiyar Manchester City Kevin De Bruyne na daga cikin yan wasa 11 da aka rairaye don lashe kyautar ya yinda a bangaren mata kuwa, ‘yar wasan Ingila da Manchester City Lucy Bronze ta samu shiga jerin wabanda ke takarar lashe kambun.

“Duk wanda zai yi adalci sannan ya san abinda ya faru a kakar da ta gabata ya san babu wanda ya cancanta kamar Lewandoski saboda kwallayen da ya zura a raga da kuma kofunan da ya lashe a kakar data gabata,” in ji kociyan na Bayern Munchen, Hansi Flick.

Ya kara da cewa “Abu ne a bayyane Lewandowski shine gwarzon duniya domin ko labari aka bawa mutum na irin bajintar da yayi yasan cewa ya cancanta da kowacce irin kyauta a duniya saboda haka muna jiran lokaci muga wanda zai lashe.”

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce za’a zabo gwarazan ne a kuri’ar da kyaftin da masu horar da kasashe a fabin duniya za su jefa bugu da kari za a ba wa wakilan gidajen jarida sama da 200 damar jefa kuri’unsu ta yanar gizo.

Za’a fara jefa kuri’ar ranar 25 ga watan Nuwamba har zuwa 9 ga watan Disamban shekara ta 2020, kafin sanar da wabanda suka lashe kyautar a ranar 17 ga watan Disambar a wani biki da hukumar za ta shirya

A wani bangaren, kwallon da ban wasan gaban Tottenham Son Heung-min ya ci Burnley na daga cikin kwallayen da ke takarar mafi kayatarwa da a ke yi wa lakabi da ‘Fifa’s Puskas Award’ kuma ita ma ta na cikin wabanda za a tantance.

A bangaren kwallon mata, ‘yar kasar Scotland Caroline Weir, mai buga wasa a Manchester City, na cikin jerin masu neman Fifa’s Puskas Award din duk da cewa a halin yanzu tana kwance tana jiyya sakamakon ciwon data samu.

 

Thiago Alcantara (Spain, Liverpool)

Cristiano Ronaldo (Portugal, Juventus)

Kevin de Bruyne (Belgium, Manchester City)

Robert Lewandowski (Poland, Bayern Munich)

Sadio Mane (Senegal, Liverpool)

Kylian Mbappe (France, Paris St-Germain)

Lionel Messi (Argentina, Barcelona)

Neymar (Brazil, Paris St-Germain)

Sergio Ramos (Spain, Real Madrid)

Mohamed Salah (Egypt, Liverpool)

Virgil van Dijk (Netherlands, Liverpool)

Caroline Graham Hansen (Norway, Barcelona)

Pernille Harder (Denmark, Chelsea)

Jennifer Hermoso (Spain, Barcelona)

Ji So-yun (South Korea, Chelsea)

Wendie Renard (France, Lyon)

 

Maza masu horarwa:

Marcelo Bielsa (Argentina, Leeds United)

Hans-Dieter Flick (Germany, Bayern Munich)

Jurgen Klopp (Germany, Liverpool)

Julen Lopetegui (Spain, Sevilla)

Zinedine Zidane (France, Real Madrid)

 

Mata masu horarwa:

Lluis Cortes (Spain, Barcelona)

Rita Guarino (Italy, Juventus)

Emma Hayes (England, Chelsea)

Stephan Lerch (Germany, Wolfsburg)

Hege Riise (Norway, LSK Kbinner)

Jean-Luc Basseur (France, Lyon)

Sarina Wiegman (Netherlands, Dutch national team).

SendShareTweetShare
Previous Post

A Na Zargin Likita Da Kashe Maradona

Next Post

Rajab Mohammad Ya Zama Shugaban Kungiyar NUJ A Jihar Yobe

RelatedPosts

United

Manchester United Za Ta Iya Bawa Duniya Mamaki

by Muhammad
3 hours ago
0

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Robert Pires,...

Zura Kwallaye

Ronaldo Yana Shirin Zama Wanda Ya Fi Zura Kwallaye A Duniya

by Muhammad
3 hours ago
0

A daren ranar Larabar data gabata dan wasa Cristiano Ronaldo...

Lampard

Ana Dab Da Korar Lampard A Chelsea

by Muhammad
1 day ago
0

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa shugabannin kungiyar ta...

Next Post
NUJ

Rajab Mohammad Ya Zama Shugaban Kungiyar NUJ A Jihar Yobe

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version