Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Frank Ribery, ya bayyana cewa dan wasan gaba na Bayern Munchen, Frank Ribery, ya bayyana cewa dan wasa Robert Lewandowski, na kungiyar ta kasar Jamus, yafi matashin dan wasa Erling Braut Haaland iya zura kwallo a raga.
A farkon wannan watan ne mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Borussia Dortmund, Lucien Febre ya bayyana cewa kawo yanzu babu dan wasa mai zura kwallo a raga kamar dan wasan gaban kungiyar, Erling Braut Haaland.
Erling Braut Haaland dai ya zura wa Borussia Dortmund kwallo 28 a wasanni 28 da ya buga mata a dukkan fafatawa kuma matashin dan wasan mai shekara 20 a duniya ya zura kwallaye biyu a ragar Club Brudge a Gasar Champions League da Dortmund ta yi nasara da ci 3-0 kafin a tafi hutun wasannin kasashe.
Kawo yanzu a cikin rukunin nasu Dortmund tana ta daya a rukuni na shida da maki shida da tazarar maki daya tsakaninta da Lazio mai biye da ita kuma manyan kungiyoyi da dama a duniya ne a halin yanzu suke bibiyar matashin dan wasan domin ganin sun dauke shi daga Dortmund din a kakar wasa mai zuwa.
Kungiyoyin Real Madrid da Manchester City da Manchester United da Barcelona da Bayern Munchen da kuma Inter Milan ne suke bibiyar matashin dan wasan wanda ake ganin kawo yanzu babu matashin dan wasa mai zura kwallo a raga kamarsa kuma duk kungiyar da zata sayeshi sai ta kashe makudan kudade.