Tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Jmie Carragha ya bayyana cewa tsohuwar ƙungiyar tasa ba za ta iya lashe kofin firimiya ba saboda batada ƙarfin ragowar manyan ƙungiyoyin da suke buga gasar.
Carragha ya faɗi hakane bayan da ƙungiyar ta Liverpool ta buga wasa canjaras (1-1) da ƙungiyar Liɓerpool a filin wasa na ST James park a ranar lahadin da ta gabata.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar bata magance matsalolin da yakamata ace tayi maganinsu ba a lokacin da ake siye da siyarwar yan wasan a watannin da suka wuce.
Yaci gaba da cewa ƙungiyar tanada matsala a yan wasan baya domin ana yawan saka musu ƙwallo a raga wanda hakan ba ƙaramar matsala bace amma ƙungiyar batayi maganin hakan ba.
Liɓerpool dai tasamu nasara ne a wasa daya acikin wasanni 7 da ta buga abinda tsohon ɗan wasan yace wannan abin kunya ne.
A cewar Carragha, idan har suna son su shiga sahun manyan ƙungiyoyi to dole sai suna lashe ƙananan wasanni da a yanzu bata iya samun nasar akansu.
Liɓerpool din dai za ta buga was anta nag aba da abokiyar hamayyar ta wato Manchester united a ranar 14 ga wannan watan a filin wasa na Anfield.