Lianhe Zaobao: Babu Wanda Zai Iya Sauya Matsayin Sin Na Zama Jagorar Masana’antu A Duniya

Daga CRI Hausa

A kwanakin baya ne, shafin intanet na “Lianhe Zaobao” na kasar Singapore ya wallafa wani sharhi, inda a cikinsa ya bayyana cewa, babu wanda zai iya sauya matsayin kasar Sin na zama jagoranta a bangaren masana’antu a duniya.

Masana sun yi imanin cewa, yanayin samar da kayayyakin kasar Sin, yana la’akari da kiyaye muhalli. Kamfanonin kasar Sin suna da tsarin gudanar da ayyukansu, amma duk da haka, suna hada kai da ma tattaunawa da juna, a don haka zai yi wahala wasu kasashe su iya maye gurbinta. Ya zuwa yanzu, tsarin samar da kayayyakin kasar shi ne mafi girma da kuma karfi a duniya.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

Exit mobile version