Likitan Talakawa, Dakta Joseph Haruna Kigbu, ya yi kira ga al’ummar Kudancin Jihar Nasarawa da su rungumi akidar zaman lafiya da junansu.
Likitan Talakawa ya bayyana haka ne a taron ranar bikin sabuwar shekara da ya gudana a gidansa da ke garin Lafia, babban birnin jihar.
Dakta Joseph Kigbu ya ce babu al’umman da za ta cigaba face sai da hadin kai da zaman lafiya tare. Ya ce dole al’umman Kudancin Jihar Nasarawa su zauna tare da juna su yafewa juna.
Dakta Kigbu yayi kira ga dukkan yan’kabilar Eggon da su zauna lafiya tare da kowa da kawo.saboda zaman lafiya shine gin shikin cigaban kowata al’umma.
Ko wani kabila na da ikon zama a ko ina cikin fadin jihar Nasarawa. Idan kuma wani yace ba zai zauna da kowa ba sai yan kabilar su to bai rungumi akedar zaman lafiya ba, wannan kuma Gwamnati zata dauki matakin ladab tarewa a kan shi.
Dakta Joseph Kigbu yayi kira ga al’umman Eggon da sauran kabilun da su kawar da kai daga siyasan kabilanci ko na addini.
Ya ce siyasan kabilanci ko na addini ba ya haifar da komai face cibaya saboda haka mutani su guji siyasan kabilanci. Su zabe mutumin da ya can canta a kowani Jam’iyya ya fito kuma kowani kabila ne .
Ya kara da cewa kada mutum ya ce sai dan kabilarsa ko wanda yake addinin sa .
Mutani su zabe wanda ya cancanta mai kishinsu mai kaunar su. Mutumin kirki wanda zai taimake su, zai kawo cigaba da samarwa matasa aikin yi.
Dakta Joseph Kigbu ya ce bamu da wata jihar da ta wuce jihar Nasarawa. Ya kamata mu rika zaben mutum na gari wanda zai kawo cigaba a jihar Nasarawa.
Taron da ya gudanar ga dukkanin ya’yan Jam’iyyun siyasa da suka hada APC PDP APGA da sauran su.