Daga Khalid Idris Doya,
Babban Daraktan Likitoci (CMD) na asibitin kwararru ta Dalhatu Araf (DASH) da ke garin Lafia, Dakta Ikrama Hassan ya shaida cewar, daga cikin Likitocinsu 139 da suke aiki a asibitin, 15 daga ciki sun kamu da cutar Korona.
Ya karyata ikirarin kungiyar Likitocin jihar da ke cewa Likitoci 35 ne suka kamu da cutar.
Da ya ke jawabi a karshen mako a Lafia, CMD, ya roki kungiyar likitocin da su amince da zaman tattaunawa da hukumar gudanarwa na asibitin DASH kan matsayarsu na rufe asibitin lura da barkewa annobar korona na biyu.
Ya na mai cewa, babban abun da ke akwai kan barkewar cutar a karo na biyu shine maida hankali sosai wajen ganin an bi hanyoyin dakile yaduwar cutar.
“Abun da muke cewa shine mu zauna mu yi magana kan abubuwan da suke akwai. Idan mutum uku sun kamu da cutar a wani sashi guda, hakan bai zama ya dace a rufe sauran sashi-sahi ba wanda babu wani guda da aka samu ya kamu da cutar a cikinsu.”
A cewarsa, hakki ne a kan hukumar gudanarwa na asibitin su tabbatar da kare ma’aikata ta hanyar samar musu da dukkanin kayayyakin kariya da za su basu damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.
Ya ce, sun dauka kuma suna kan daukan matakan da suka dace wajen kula da lafiyar majinyata ba tare da cutar da masu aiki ko shafar ma wasu cutar da suke dauke da su ba.
Ya ce, sun bada shawarorin dukkanin matakan kariya daga cutar ake bin su.