Muhammad Maitela" />

Likitoci Sun Gargadi A Kan Ba Kananan Yara Maganin Maleriya Barkatai

Kwararren likitan cutukan kananan yara, Dakta Okunola Olusola, ya gargadi iyaye dangane da bai wa kananan yara magungunan ‘anti-malaria’, alhalin kwararrun likitoci ba su gudanar da gwajin da ya tabbatar da cewa yaran suna dauke da zazzabin maleriyar ba.
Mista Olusola, wanda kwararren likita ne wanda yake aiki a sashen kula cutukan kanan yara ‘Paediatrics Department’ a asibitin koyarwa da ke jami’ar Benin (UBTH), shi ne ya yi wannan gargadin, a wata tattaunawar da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a birnin Legas.
Ya bayyana cewa babban kuskure ne a rinka baiwa kananan yara kwayar maganin ‘anti-malaria’ kara-zube, wanda tana iya yuwa ba su dauke da cutar maleriya, tare da karin hasken cewa yin hakan zai haifar da wani lahani a lafiyar su (ailment).
“Wanda yin hakan shi ake kira shan magani ba bisa ka’ida ba, kuma shi yake baiwa wasu cutaka masu lahani a jikin dan adam dama wajen habaka da bijirewa wasu magunguna, idan an yi amfani dasu lokaci bayan lokaci”.
“Saboda haka, abinda yakamata iyaye su yi shi ne, a duk lokacin da aka gano yaro yana fama da zazzabi, su dauke shi zuwa cibiyar kiwon lafiya wadda ta cancanta domin gudanar da gwaje-gwajen maleriya”.
“Wanda akwai na’urorin gudanar da gwajin cutar maleriya ga kananan yara, da yawa a asibitoci (RDTS), wanda cikin mintuna 10 zasu bayar da sakamako. Wanda kuma su ne kayan gwajin da zasu taimaka wa a gano maleriyar a cikin jinin mutum- wadanda basu da wata tababa’’. Inji shi.
Likitan kananan yaran ya sake ankarar da iyaye mata da cewa, yana da kyau su fahimci cewa ba kowanne zazzabi ne yake da alaka da maleriya ba, yayin da wani zazzabin yana zuwa ne ta dalilin fitar hakorin yara da makamantan su.

Exit mobile version