Daga Abubakar Abdullahi, Lafiya.
Hadakar kungiyoyin ma’aikatan kiwon lafiya reshen cibiyar kiwon lafiya ta tarraya da ke Keffi a Jihar Nasarawa, sun bi bayan takwarorinsu na tarraya inda suka shiga yajin aikin sai baba-ta-gani tare da umurtar ma’aikatan da suka yi kunnen uwar hegu suka je wurin aiki da su koma gidajensu. Shugaban hadin gwiwar ungiyoyin, Achimugu Isiah ne ya sanar da haka sa’ilin da yake jawabi ga ‘yanjaridu a wannan mako a garin Keffi da ke jihar.
Isiah ya ce, sun amince su shiga yajin aikin ne domin bin umarnin uwar kungiyar su ta kasa. Tare da cewa babban aikin ma’aikacin kiwon lafiya shi ne, tabbattar da inganta jin dadi da walwalar marasa lafiya, to amma ma’aikatan kiwon lafiya sun kasance ba su da zabi illa iyaka su shiga yajin aiki domin su ma a inganta jin dadi da walwalarsu.
Ta bakinsa, “Mun kira taron ‘yanjarida ne domin sanar da marasa lafiya da sauran al’umma dalilinmu na shiga yajin aikin, mun shiga yajin aikin ne saboda kishin jama’a musamman ma talakawa”. Ya ci gaba da cewa, “Wa’adin kwanaki bakwai da uwar kungiyarmu ta bai wa gwamnati ya kare, hakan ya sa muka shiga yajin aikin, saboda haka muna sanar da jama’a da su kara hakuri da mu saboda ba za su san dalilinmu na shiga yajin aikin ba”.
Har wa yau ya ce, “Gwamnatin Tarraya ta gaza biya mana wasu daga cikin bukatunmu da suka hada da kara shekarun barin aiki na ma’aikatan daga sittin zuwa saba’in da biyar da bai wa asibitocin koyarwa ‘yancin cin gashin kansu. Haka nan karanci kudaden gudanarwa ga asibitoci na daga cikin abubuwan da suka sa aka shiga yajin aikin, muna bukatar gwamnati ta duba yiwuwar yin gyara ga batutuwan karin girma da albashi da sauransu”.
Bugu da kari, Isiah ya ce samar da kudade gudanarwa ga asibitoci zai taimaka nesa ba kusa ba wajen inganta jin dadi da walwalar ma’aikata da kuma hana ma’aikata zuwa aiki sai lokacin da suka ga dama.
A nasa dangaren, babban shugaban cibiyar, Dakta Joshua Giyan kira ya yi ga ma’aikatan da su yi hakuri su dawo bakin aiki domin taimaka wa marasa lafiya.