Connect with us

KIWON LAFIYA

Likitoci ‘Yan Nijeriya 5,000 Ke Aiki A Kasar Afrika Ta Kudu –inji Ambasada

Published

on

Babban jami’i a ofishin jakadanci na kasar Afirka ta Kudu dake Nijeriya Mista Godwin Adama ya sanar da cewar, kimanin ‘yan Nijeriya kwararrun kiwon lafiya su 5,000 ne sauke gudanar da aikin kiwon lafiyar a kasar sa.

Mista Adama ya sanar da hakan ne a sanarwar da mataimakin sashen yada labarai da aladu na ofishi Dabid Abraham ya bai wa kamfanin dillancin labarai na kasa a ranar Litinin data gabata a Abuja.

Mista Adama ya sanar da hakan ne a lokacin da kungiyar dake kasar sa ta kai masa ziyara da Sakataren kungiyar Emeka Ugwu, ya jagoranci tawagar likitocin,inda ya kara da cewar maaijatan kiwon lafiyar na Nijeriya suna yin aiki a asibitoci masu zaman kansu da kuma na gwamnati a kasar sa.

Ya yi nuni da cewa, wannan ya nuna cewar, a dukkan daukacin asibitocin kasar na gwamnati da kuma masu zaman kansu akawai yan Nijeriya da suke yin aiki kuma hakan ya nuna cewar suna bayar da taau gudunmawar wajen ciyat da kiwon lafiya na kasar tamu.

Sai dai ya nuna takaicin sa akan yadda kafafen yada kabarai basu kawo rahoto akan hakan.ya kuma kara da cewar, kwararrun na kiwon lafiya na Najeriya dake Afirka ta Kudu.suna kuma taimakawa gajiyayyu musamman ga yan Najeriya dake zaune a kasar.

A karshe ya ce, ofishin jakadancin zai ci gaba da yjinjinawa likitocin Nijeriya

Da sauran kwararrun kiwon.lafiya dake kasar ta Afirka ta Kudu kuma ofishin zai ci gaba da yin hadaka da kungiyar likitoci ta Nijeriya dake kasar Afirka ta Kudu don.inganta rayuwar yan Nijeriya.

 

 

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: