Muazu Hardawa" />

Limamin Bauchi Ya Shawarci Maniyyata Su Tsarkake Niyyarsu Tare Da Yi Wa Kasa Addu’a

Babban limamin masallacin Bauchi Alhaji Bala Ahmad Baban Inna, ya shawarci maniyyata aikin hajjin bana musamman wadanda  suka fito daga jihar Bauchi da su tsarkake niyyarsu a yayin tafiya ibadar aikin hajji don samun ayyuka karbabbu da za su sa a amshi dukkan addu’o’in da suka gudanar a yayin da suke kasa mai tsarki.

Alhaji Bala Ahmed ya bayyana hakaa ne cikin hirarsa da wakilinmu a Bauchi, inda ya kara da cewa yin wannan kira ya zamo dole domin tunatar da jama’a su lura da makudan kudin da suka kashe don tafiya sauke farali a bana. Saboda bai dace ba mutum ya kashe kudi masu yawa don yin wannan tafiya ta ibada amma ya sake wajen yin wasu ayyuka da za su haifar da nakasu game da karbar ayyukansa.

Don haka ya ja hankalin maniyyatan da su gabatar da ibada mai kyau ta hanyar tsarkake niyya da nisantar  maganganu da ke lalata ayyukan Hajji ta hanyar nisantar yin munanan maganganu ko yasasshiyar magana da sauran ayyuka munana wadanda ke bata aikin Hajjin da aka yi takakkiya don aiwatarwa da nufin samun gafarar Allah madaukakin Sarki.

Babban limamin na Bauchin har wa yau ya roki maniyyatan da su doge wajen yi wa Nijeriya addu’ar samun inganyaccen zaman lafiya da yalwar arziki. Musamman a wannan lokacin da lamurra na zubàr da jinin bayin Allah ke kara yawaita a wasu sassa na kasar nan. Don haka  akwai bukatar maniyyata su himmatu wajen yin addu’a domin Allah ya kawo saukin abin da ke faruwa da kuma yalwar arziki a kasar nan, don jama’a su fita daga cikin kuncin rayuwa da ake fama da shi a wannan lokacin.

 

Exit mobile version