Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Limamin Coci Ya Fadi Matacce A Na Tsaka Da Ibada

by
2 years ago
in JAKAR MAGORI
2 min read
Limamin Coci Ya Fadi Matacce A Na Tsaka Da Ibada
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Wani Malamin Coci ya yanke jiki ya fadi matacce a lokacin da yake cikin wa’azi a Douala, kasar Kamaru. A cikin wani bidiyo da Chidi Odinkalu ya wallafa, ya dan huta kadan kafin ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake cikin wa’azi. Masu amfani da shafin Soshiyal Midiya sun je shafin Twitter domin fadin ra’ayinsu kan al’amari na bakin ciki da ya afku a kasar ta Kamaru, lokacin da aka sanar da labarin wannan limamin coci mai suna Father Jude ya yanke jiki ya fadi matacce a lokacin da yake wa’azi.

Wani tsohon Shugaban hukumar kare hakkin bil’adam na kasa, Chidi Odinkalu ne ya wallafa bidiyon a shafin Twitter. Odinkalu ya rubuta: “Rabaran. Fr Jude., CMA, Daraktan CMA Deido, a babbar birnin Kamaru, Douala, na tsaka da wa’azi a cikin dandazon al’umma a yau lokacin da wannan faru. Allah ya jikan shi.” Mutumin, wanda ya kasance sanye da takunkumin fuska, ya dan dakata na dan lokaci sannan ya yanke jiki ya fadi. Sauran limaman cocin sun yi gaggawan kai masa agaji amma ya mutu. Reberend Father Jude ya kasance daraktan kungiyar limaman Katolika a Douala, kasar Kamaru.

Wasu masu amfani da shafin Twitter sun bayyana ra’ayinsu game da lamarin. Wani mai amfani da Twitter @OYEDEJI ya rubuta: “Shin kun lura wani mutum na share gumi daga fuskarsa saboda dakin ya dauki dumi, sannan kuma ga takunkumin fuska a sanye. Eh, tabbass yana da muhimmanci. Shi ya sa zan cire takunkumin fuskata idan na ga bana iya numfashi da kyau idan ina sanye da shi. Rai daya ne!”

Labarai Masu Nasaba

Yadda Shark Ya Hadiye Mai Ninkaya Tsawon Dakika 30 Kafin Ya Amayo Shi

Kotu Ta Tsare Mutum Shida Bisa Laifin Kisan Kai

Da yake martani ga @OYEDEJI, @dibergentscou ya rubuta: “Takunkumin fuska ba zai zama ainahin abin da ya haddasa hakan ba, amma na amince da kai, yana iya kasancewa daga cikin abin da ya haddasa hakan.

“Na lura da idonsa sau da dama, akwai alamu sosai da suka nuna faruwan haka. Allah ya ji kansa. Sanya takunkumin fuskarka. Ka tsira.”

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

An Tsare Shugaban Otel Rwanda Mai Adawa Da Kagame

Next Post

Oshiomole Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Mummunan Hatsarin Mota

Labarai Masu Nasaba

Shark

Yadda Shark Ya Hadiye Mai Ninkaya Tsawon Dakika 30 Kafin Ya Amayo Shi

by
8 months ago
0

...

Kotu

Kotu Ta Tsare Mutum Shida Bisa Laifin Kisan Kai

by
9 months ago
0

...

Gwamnan Jihar Adamawa

An Daure Wani Dan Kasuwa Saboda Cin Mutuncin Gwamnan Jihar Adamawa

by
9 months ago
0

...

EFCC

EFCC Ta Gurfanar Da Wanda Ake Zargi Da Damfarar Naira Miliyan 425 Ta Intanet A Gaban Kotu

by
9 months ago
0

...

Next Post
Tsakanin Gwamnonin APC Da Adam Oshimole Wa Zai Ga Bayan  Wani?

Oshiomole Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Mummunan Hatsarin Mota

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: