Limamin Ka’aba Ya Ziyarci Gwamna Zulum Na Jihar Borno

Gwamna Zulum

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

Limamin Masallacin Harami (Ka’aba Mai Tsarki) da ke birnin Makkah ta kasar Saudi Arabia, Farfesa Hassan Abdulhamid Bukhari, ya ziyarci Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Maiduguri, da yammacin Laraba.

Farfesa Bukhari, shi ne shugaban sashen koyar da harshen Larabci a jami’ar Ummul Kura da ke birnin Makkah, ya kai ziyara a Maiduguri a karkashin gayyatar Dr. Mohammed Kyari Dikwa, shugaban gidauniyar ‘Al-ansar Foundation’ wadda ke gina jami’a mai zaman kanta ta farko a jihar Borno, mai mazauni a Maiduguri.

Limamin massalacin Ka’abar, a sa’ilin da yake ganawa da Gwamna Zulum, ya bayyana cewa yanayin karimcin al’ummar jihar Borno ya yi matukar bashi sha’awa tare da dogon tarihin ilimin Al-kur’ani Mai Girma da al’ummar jihar suka shahara dashi, wanda ya ce jihar ta yi fice a fannin karatun Al-kur’ani a fadin duniya baki daya.

Professor Bukhari, whose message was translated into English by his host, Dr Dikwa, noted that he was happy to associate with Zulum’s administration habing monitored all his achiebements in far away Saudi Arabia.

“A kebance, Farfesa Bukhari ya nuna farinciki dangane da kokarin da kake yi, saboda yadda ya dade yana bibiyar hubbasar da kake yi a shekarun da suka gabata, kuma ya na farincikin hada hannu da kai tare da gwamnatin ka bisa ga ayyukan ci gaba da kake kokarin aiwatar dasu cike da himma.” Kamar yadda Dr. Dikwa ke fassara kalaman malamin.

A nashi bangaren, Gwamna Zulum ya shaidar da cewa akwai dogon tarihin alaka tsakanin jihar Borno da kasar Saudi Arabia, musamman a kan wakilcin masallatai biyu masu tsarki, kana ya bayyana godiya dangane da wannan ziyarar.

“Matukar abin alfahari ne, daya daga cikin limaman masallaci Mai Tsarki, Masallacin Harami ya ziyarci birnin Maiduguri abin farinciki ne ga baki dayan musulmin wannan jihar.” In ji Zulum.

Haka kuma ya nemi goyon bayan gwamnatin kasar Saudi Arabia wajen koyar da ilimin Larabci da na addinin musulunci a jihar. Har wala yau kuma, Zulum ya bukaci cikakken goyon kasar wajen canja tsattsaurar akidar tayar da zaune tsaye a kokarin da jihar keyi na samun dawamamen zaman lafiya a jihar Borno.

A karshe Gwamnan ya yi karin hasken cewa asalin Kanuri sun fito ne daga kasashen Larabawa kafin yada zango zuwa Borno.

Exit mobile version